Home Siyasa Muna so a dakatar da sanar da sakamakon zaɓe – Kwamitin yakin...

Muna so a dakatar da sanar da sakamakon zaɓe – Kwamitin yakin zaɓen Atiku

213
0

Kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar ya yi fatali da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na Najeriya da ake ci gaba da fitarwa, inda ya yi kira da a ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammalu ba.

A cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar wanda ya samu sa hannun mai magana da yawun ta dakta Daniel Bwala, ta ce hukumar zaɓe ta dakatar da karɓa da kuma sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da ta ke yi.

Daniel Bwala ya ce dakatar da karɓar sakamakon ya zama tilas don shawo kan matsaloli da jam’iyyu suka yi korafi a kai dangane da rashin amfani da na’urar BVAS da kuma kasa tura sakamakon zaɓen zuwa shafin INEC.

Sanarwar ta ce abin da ya kamata INEC ta yi a yanzu shi ne sanya sabon ranar gudanar da zaɓe a wuraren da aka fuskanci matsalar, tare da tabbatar da cewa an aika sakamakon zuwa shafin yanar gizo na hukumar zaɓe.

Sanarwar kwamitin ya ƙara da cewa a soke dukkan sakamakon zaɓen da aka sanar har sai lokacin da aka aika sakamakon da aka tattara a rumfunan zaɓe zuwa shafin INEC.

Kwamitin ya kuma ce INEC ta fito ta yi wa ‘yan ƙasa jawabi kan sahihancin zaɓe da ta gudanar don samun ƙwarin gwiwa daga ‘yan ƙasar da ma al’ummomin ƙasashen waje. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here