Home Ilimi Muna Bukatar Dalar Amurka Biliyan 1.6 Don Mayar Da Yara Miliyan 14...

Muna Bukatar Dalar Amurka Biliyan 1.6 Don Mayar Da Yara Miliyan 14 Makaranta – Hon. Sharada

243
0
Hon. Sha'aban Sharada

Hukumar nan ta Kasa da ke Kula da Almajiri da kuma Yara wadanda ba sa zuwa makataranta ta ce ta na bukatar tsabar kudi kimanin Dalar Amurka Biliyan daya(1) da Miliyan dari shida (6) domin ceto yara Miliyan 14 da ba sa zuwa makaranta.

 

Shugaban Hukumar, Hon. Sha’aban Sharada ne ya sanar da haka ranar Talata bayan sun zauna da Kwamiti na Majalisar Wakilai da ke kula da Wannan Ilimi na musamman domin lalubo mafita ta yadda za a ceto wadannan yara da ga fadawa miyagun laifuka.

 

Hon. Sharada ya ce makasudin zaman na su shi ne domin su fahimci juna tsakanin Hukumomi da suke karkashin Kwamitin da su Yan Kwamitin a wani mataki na lalubo mafita wajen ganin an ceto wadannan yara da ga halaka.

 

Shugaban Hukumar Almajiran ya ce sun gamsu da yadda Kwamitin ya nu na damuwar sa na ganin ya tallafawa ma’aikatun ta hanyar gaiyato kwararru akan hankar tare da ne mo ma su sha’awar bayar da agaji ga Hukumomin.

 

Hukumomin da za su ci gajiyar wannan shiri sun hada da Hukumar Almajirai da wadanda basa zuwa makaranta da Hukumar Kula da Ilimin Makiyaya da Kuma Hukumar Ilimin Manya.

 

Hon. Sharada ya ce sun fito da tsare-tsare wadanda suke ganin za su tallafawa wadanda ba sa zuwa makaranta ta hanyar basu ilimi na zamani da na addini tare da koya mu su sana’o’I domin su dogara da kansu.

 

Ya ce fatan su shine ace yarannan sun sami rayuwa mai inganci ta hanyar samun abinci ba sai sun yi bara ba da samun wurin kwana mai kyau da kuma matsuguni da za su rinka bahaya da sauran bukatu na rayuwa ma su kyau.

 

Da ga karshe Hon. Sharada ya yi kira da masu kudi da Yan boko da Yan Kasuwa da Malamai da Sarakuna da su tallafawa wannan shiri ta hanyar ba shi goyon baya da shawarwari da ma kudi domin mayar da wadan nan yara zuwa makaranta.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here