Home Uncategorized Mun Karawa Alkalai Albashi Kaso 300 Ne Don Mu Raba Su Da...

Mun Karawa Alkalai Albashi Kaso 300 Ne Don Mu Raba Su Da Kwadayin Kayan Hannun Mutane – In ji Majalisar Dattawa

66
0
Senator Maidoki

Majalisar Dattawa ta ce dalilin ta na karawa Manyan Alkalai Albashin har linki kashi 300 wani mataki na kawo karshen cinhanci da rashawa da dawo da martabar Doka da oda a Kasarnan.

Sanata Garba Musa Mai Doki Dan Majalilar Taraiya da ke Wakiltar Jihar Kebbi ta Kudu ne ya sanar da haka a hirar sa Yan Jaridu a ofishin sa da ke Abuja a ranar Alhamis.

Ya ce sun lura cewa, Alkalai su ne gatan maras karfi amma albashin su ba zai iya biya mu su bukatun su ba na zirga-zirga balantana sauran bukatun su na rayuwa, sabo da haka idan a na so su tsaya suyi aikin su kamar yadda ya kamata ba sani ba sabo sai an yi mu su albashi da zai dauke hankalin su da ga kwadayin abun hannun mutane.

Sanata Mai Doki wanda ya nuna takaicin sa na halin da bangaren shari’a ya shiga na cinhanci da rashawa da tabarbarewa al’amura sakamakon rashin bin doka da oda wanda ya ce duk matsalolin da ake fama da su su na da alaka da rashin bin doka da oda. Sabo da haka ne su ke ganin mataki na farko shi ne a gyara albashin alkalai ta yadda za su rinka gudanar da aikin su ba sani ba sabo.

Bayan haka ya nuna goyan bayan sa na karawa dukkan ma’aikatan Najeriya albashi domin shi ne kashin bayan da zai bawa ma’aikaci dama ya gudanar da aikin sa cikin gaskiya da rikon amana.

In da ya kawo misali da irin albashin da ake biyan ma’aikata a kasashen waje na Dalar Amurka 20 kowacce awa. Wanda ya ce a Najeriya ma ya kamata ta rinka biyan ma’aikatan ta da Dalar Amurka tun da kudaden shigar da su ke shigowa Kasar da ita Dalar ake biyan ta.

Ya ce aikin Gwamnati ya lalace in da ya ce a halin yanzu ma’aikata ba sa iya zuwa ofis kullum sabo da tsadar rayuwa a sakamakon haka Majalisar a shirye ta ke ta goyi bayan karawa ma’aikata albashi da zarar Kudurin bukatar hakan ya zo gabanta.

A wani bangaren kuma Sanata Mai Doki ya nuna takaicin sa game da matsalar Tsaro da ta addabi yankin Arewa in da ya ce a matsayin sa na manomi Yan ta’aadda sun hana shi yin noma da kiwo a yankin sa na Jihar Kebbi.

Ya ce a duk shekara ya na noma buhun masara sama da guda dubu kuma ya na da shanu sama da guda dubu amma Yan ta’adda sun hana shi noma kuma sun kore dukka shanun da ya mallaka wanda ya ce hakan wata babbar matsala ce da zata kara ta’azzara matsalar tsaro a Kasarnan domin abinci shi ne bukata ta farko ga kowanne mutum.

Sanatan ya kara da cewa ya san Gwanati ta na yin kokari ta fannin Tsaro amma akwai bukatar a sake daukar matakai da za su kawo karshen wannan matsala domin rashin abinci ka iya ta’azzara matsalar tsaron ta shafi sauran yankunan da ake ganin akwai zaman lafiya a halin yanzu.

A bangaren noma ma ya bukaci Gwamatin Taraiya da sauran gwamnatoci da su rinka tallafawa manoma da iri da taki da kayan noma. In da ya ce a duk duniya ana bawa manoma tallafi sabo da irin gudunmawar da suke bayar wa wajen samar da zaman lafiya da bunkasar tattalin arzi.

Mai Doki wanda y ace yasan Gwamnati tana bayar da tallafi na noma amma baya kaiwa ga manoma na gaskiya. Sabo da haka ya bukace ta data fito da tsari shigen wanda tsohon Ministan Noma ya fito das hi na bawa manoma taki ta wayar salula wanda y ace haka ya tallafa mutuka wajen inganta noma a Kasarnan,

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here