Home Siyasa Mukamin Minista: Ko Elrufa’i da Wike Sun Lashe Amansu?

Mukamin Minista: Ko Elrufa’i da Wike Sun Lashe Amansu?

183
0
eLRUFAI AND WIKE

Tun dai bayan da sunayen tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Elrufai da na tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike suka bayyana a jerin sunayen ministocin da Shugaba Tinubu ya aike wa da majalisar dokoki domin tantancewa ‘yan Najeriya suka yi ta sukar tsaffin gwamnonun.

Ana dai ta sukar Elrufai da Wike ne kan wadansu bidiyonsu da suka yi ta wadari a intanet, inda kowanne a cikinsu ya cika baki cewa ya fi karfin kujerar minista.

Shi dai Elrufai ya ce “Na yi ministan Abuja ina shekara 43. to sai kuma bayan shekara 20 sai na sake karbar minista? Sai ka ce ba ka da kanne da ‘yan uwa da wadanda ka bai wa horo. Kenan babu wanda zai iya yi. Hakan ai gazawa ce ‘

Shi ma tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyeson Wike a lokacin wani gangamin yakin neman zabe a bara ya ce ” Kowacce jiha dai mutum daya ne zai zama minista. Ni kuwa ba zan yi minista ba. Ba zan yi ba saboda ni ba kaska ba ne. ”

Tuna baya…

Malam Nasir Elrufai dai ya yi ministan babban birnin tarayya Abuja daga 2003 zuwa 2007.

Shi ma tsohon gwamnan jihar ta Rivers, Nyesom Wike ya rike karamin ministan ilimi daga 2011 zuwa 2014.

Sharhi

Masana kimiyyar siyasa dai na yi wa wannan al’amari kallon halayyar ‘yan

siyasa ta ‘fada ba cikawa ‘.

Dr Abubakar Kari wanda malami ne a jami’ar Abuja ya ce ” wannan ai ba wani abu ne daban ba illa halayyar ‘yan siyasa .”

” Hatta mutumin da ake yi wa kallon mai gaskiya wato Muhammadu Buhari ya yi irin wannan inda a 2011 ya ce ba zai sake tsayawa takarar shugaban kasa ba amma daga karshe har karo na biyu ya nema,” in ji Dr Kari.

Masanin kimiyyar siyasar ya kara da cewa ” shi ma Obasanjo haka ya yi amma ya buge da neman tazarce karo na uku.”

Dr Kari ya kara da cewa ‘akwai yiwuwar tsoffin gwamnonin biyu sun samu matsin lamba wajen shawo kansu su yi wurgi da ra’ayin nasu na baya na kushe kujerar minista.” (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here