Home Siyasa Ministocin Tinubu: Wace ce Maryam Shetty Da Ga Kano ?

Ministocin Tinubu: Wace ce Maryam Shetty Da Ga Kano ?

273
0
Maryam Shetty 1

A ranar Laraba ne shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya aika da jeri na biyu na sunayen mutanen da yake so Majalisar Dokokin ƙasar ta tantance domin naɗawa a matsayin ministoci.

A cikin jerin sunayen akwai tsofaffin gwamnonin jihohi, da ƴan majalisa da kuma matasa.

Daga cikin matasan da ke cikin jerin sunayen ya ƙunshi, wacce ta fi ɗaukar hankali ita ce Maryam Ibrahim Shettima daga jihar Kano.

Wace ce Maryam Ibrahim Shettima?

An haifi Maryam Shettima Ibrahim wacce aka fi sani Maryam Shetti ce a jihar Kano, a shekarar 1979.

Maryam Shetty 2

Jika ce ga Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero kuma Yar Uwace ga Sarkin Kano na Yanzu, Alhaji Aminu Ado Bayero da Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero.

Ta yi karatu na Firamare da Sakandare a Kano sannan ta yi digirinta na farko a jami’ar Bayero da ke Kano, inda ta yi karatu a fannin lafiya, inda ta ƙware a fannin gashi.

Ta yi aiki da asibitin Kashi na Dala da Asibitin Malam Aminu Kano kafin dag a bisani ta tafi karo karatu wato digirinta na biyu a jami’ar Stratford da ke Birtaniya inda ta karanta fannin kula da ƙashi na ɓangaren wasanni.

Maryam ta kasance a cikin likitocin tawagar Najeriya a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya da aka gudanar a birnin Landon a shekara ta 2012.

Baya ga wannan, Maryam ta yi kwasa-kwasai da dama a wasu cibiyoyi na ƙasashen duniya, ciki har da Amurka.

Duk da cewa ba ta taɓa yin takara ba, ta kasance ƴar siyasa a a jam’iyyar APC mai mulki.

Ta kasance a cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen Gawuna/Garo da na shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.

Kuma shahararriya ce a shafukan sada zumunta na Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here