Home Siyasa Ministoci 48 Sunyi Yawa, Ba Lallai Majalisar Taraiya Ta Amince Da Su...

Ministoci 48 Sunyi Yawa, Ba Lallai Majalisar Taraiya Ta Amince Da Su Duka Ba – Inji Sanata Hanga

172
0
Sen. Hanga

Tantancewa ba ya na nufin Majalisar Dattawa zata amince da dukkan jerin sunayen Ministoci 48 da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya aike da su gaban Majalisar Dattawa ba lura da irin halin da kasar take ciki na matsi na tattalin arzikin kasa.

Sanata Rufai Hanga ne ya ja hankalin Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu akan yawan Ministocin da ya bayar 48 inda ya ce sunyi yawa lura da yanayin da kasar take ciki na matsi na tattalin arziki da kuma irin makuden kudaden da za a rinka kashewa akan su.

“wannan ra’ayi na ne, a ka’ida sunanayen Ministoci 36 Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya ce; amma Ministoci 48 sunyi yawa lura da halin da kasarnan ta ke ciki”

Sanata Hanga ya ce, nada Ministoci 48 na nufin daukar nauyin su dana hadimansu dama daukar dukkan dawainirsu na motoci da kayani aiki; hakan almubazzaranci ne, idan akayi la’akari da halin da kasarnan take ciki.

Ya ce sabo da haka idan sunzo amincewa da jerin sunayen Ministocin ranar Litinin za suyi wadannan tambayoyi, na irin makuden kudade da za a kashe akan su; idan Majalisa ta amince shikenan ko akasin hakan.

A kan batum canza Maryam Shetty da Mariya Bunkure a jerin sunayen ministoci da ga Kano da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya yi  ya ce ba ita kawai aka canza ba an canza wasu kafin a sanar a zauren Majalisar.

“sau biyu aka yi canji a zauren Majalisa, na farko kafin a sanar a zauren Majalisa; na biyu bayan an sanar. Kai harma bayan mun buga sunan Maryam Shetty a jadawalin aiyukan mu na wannan rana” inji Hanga.

Hakan bai dace, kamata ya yi karma a kawo sunayen Majalisar sai bayan an cire duk wanda ake so a cire. Amma yin hakan bai dace ba, kuma ya sabawa tsarin Majalisar inji Sanata Hanga.

Sanata Hanga ya kara da cewa bai dace ba a sauya sunan Yar talaka da sunan wadda ta ke da uwa a gindin murhu. “ na sami labari cewa Mariya Bunkure da aka canza da Maryam Shetty yarinya Gwaggo ce, matar Shugaban Jam’iyar APC, Abdullahi Ganduje wanda hakan bai dace ba”

Hon. Muktar Dahiru Gora, Shugaban Kungiyar Cito APC, a Yankin Arewa Maso Yamma ya nuna rashin jindadinsa na yadda aka Canza Maryam Shetty da Mariya Bunkure idan hakan bai d ace ba domin zai sanyaywa matasa gwiwa na bayar da gudunmawarsu a siyasa.

Hon. Gora

Ya ce duk da yake ba a san Maryan Shetty a siyasar Kano so sai amma ta bayar da gudunmawa wajen kawo Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinuba muassamman a shafikan sada zumunta da sauran tarurrukan siyasa.

Hon. Gora ya ja hankalin Mariya Bunkure da ta tsaya da kafafunta wajen ganin tayiwa kasarnan aiki da Jihar Kano ba wait a zama Karen farautar wadanda ake zargi su suka ba da sunanta a jerin sunayen Ministocin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here