Home Siyasa Me ya sa PDP ta kasa hukunta Nyesom Wike?

Me ya sa PDP ta kasa hukunta Nyesom Wike?

153
0
Wike

Rahotanni na cewa shugaban babbar jam’iyyar hamayya ta Najeriya, PDP, Ambasada Iliya Damagum, na fuskantar gagarumin matsin-lamba daga wasu manyan jam’iyyar don hukunta tsohon gwamnan jihar Ribas, kuma ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, kan zargin yi wa jam’iyyar zagon ƙasa.

Shi dai Wike wanda har yanzu bai sanar da sauya sheƙa daga jam’iyyar ba ya nuna goyon bayansa ne ga Shugaba Tinubu na APC a fili a zaɓen shugaban ƙasar da ya gabata,har ma ya karɓi muƙamin minista a gwamnatinsa, kana daga bisani ya ci gaba da yin abubuwan da wasu ke kallo a matsayin cin dunduniyar jam’iyyar.

A baya-bayan nan ne wasu ‘yan majalisar dokoki 27 na jihar ta Ribas makusantansa, suka fice daga PDP zuwa APC, wani abu da wasu ke kallo a matsayin sharar fage ga shi ma Wiken.

Bayanan da BBC ta samu daga wasu gaggan jam’iyyar ta PDP har da ‘yan kwamitin gudanarwarta, sun nuna rashin jin dadinsu, a kan jinkirin da ake samu, wajen ɗaukar mataki a kan Nyesom Wike.

Kiraye-kirayen sun ƙara ƙamari bayan ganawar da Shugaba Tinubu ya yi da Wiken da magajinsa, da zummar warware rikicin siyasar da ya ɓarke a tsakaninsu, duk da cewa shi dan APC ne, su kuma ƴan PDP, abun da wasu jagororin jam’iyyar ke nuna wa shugabancinta cewa wannan nakasu ne ga PDP.

To sai dai an ruwaito shugaban na PDP Ambasada Iliya Damagun, na neman a dan ƙara haƙuri, bisa kyautata zaton cewa Wike, zai sassauta ya mayar da wukarsa cikin kube.

Malam Ibrahim Abdulahi, wanda shi ne mataimakin kakakin jam’iyyar ta PDP a Najeriya, ya tabbatar wa BBC da tayar da jijiyar wuyan da wasu ƴa’ƴan jam’iyyar ke yi kan wannan batu.

Ya kuma ce wasu daga cikin waɗanda ke da alhakin dauƙar mataki kan batun, ba sa goyon bayan dauƙar mataki a yanzu.

“Kwamitin gudanarwa yana aiki kan matakin da ya dace sai dai akwai wasu da ba su gamsu a ɗauki mataki ba, inda suke ganin a ƙara ba shi lokaci a gwada imaninsa domin a gano idan manufarsa ta cuta wa jam’iyya ce, ” cewar Malam Ibrahim.

Farfesa Kamilu Sani Fagge, masanin harkokin siyasa ne a Najeriya ya kuma shaida wa BBC cewa, “jam’iyyar PDP ta yi wa Wike riga da wando, domin ya faro daga shugaban ƙaramar hukuma har zuwa matakin gwamna, don haka inda wani ne shi , da sai ya zauna cikin jam’iyyar ko kuma idan bai gamsu ba ya fita.”

“Har kuma yake bugun ƙirji yana cewa ba a isa a hukunta shi ba, inda PDP, jam’iyya ce mai ɗa’ar cikin gida da tuni ta hukunta Wike, musamman idan aka yi la’akari da yadda ya fito a fili yana waƙoƙin yabon Shugaba Tinubu, “in ji masanin siyasar.

Jam’iyyar PDP dai ita ce babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, sai dai masana na ganin irin wadannan rikice-rikice da take fama da su na haifar mata da babbar barazana, a yayin da wasu ƙananan jam’iyyu ke samun goyon bayan jama’a.

To sai dai wasu jagororin jam’iyyar na ganin cewa ba wannan ne farau ba, don haka yanzu ma za ta farfaɗo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here