Home Cinikaiyar Zamani Me ya sa ake ƙarancin takardun naira yanzu a sassan Najeriya?

Me ya sa ake ƙarancin takardun naira yanzu a sassan Najeriya?

146
0
NAIRA Taru

‘Yan Najeriya da dama, musamman masu sana’ar cire kuɗi ta na’urar POS, na ci gaba da kokawa game da ƙarancin takardun naira da ake fama da shi a faɗin ƙasar.

Wannan na ci gaba da faruwa ne, duk da yadda Babban Bankin Najeriya CBN ya sha musanta batun ƙarancin kuɗi a lalitarsa, yana mai ɗora wa bankunan kasuwanci da ‘yan ƙasa laifin cirar tsabar kuɗi fiye da kima.

‘Yan POS na cewa bankuna sun rage kuɗaɗen da suke ba su sosai, ta yadda ba sa iya samun ko kashi 10 cikin 100 na abin da suka saba samu.

Kusan shekara guda ke nan da ‘yan Najeriya suka fara fuskantar tsananin ƙarancin takardu naira, lokacin da gwamnatin ƙasar ta sauya fasalin manyan takardun da kuma rage yawansu a hannun jama’a.

Duk da cewa yanayin na yanzu bai kai kusa da na shekarar 2022 ba, ana ganin lamarin yana ƙara ta’azzara ne saboda ƙaratowar bukukunwan ƙarshen shekara.

Masana harkokin kuɗi da masu sana’ar POS da dama sun ɗora alhakin ƙarancin kuɗin a kan bankuna, da kuma ‘yan kasuwa.

‘Daga 500,000 zuwa 50,000’

‘Yan Najeriya da dama na ci gaba da dogara da masu POS wajen cirar kuɗi domin biyan buƙatunsu a harkar saye da sayarwa, duk da yawan na’urorin cirar kuɗi na ATM da ake da su a lungu da saƙo na ƙasar.

CBN ya ɓullo da tsarin hada-hada ta POS a hukmance da zimmar rage jigilar garin kuɗi a fili, da kuma taimakawa wajen rage hulɗa da takardun don komawa tsarin hada-hada ba tare da takardun ba – watau tsarin cashless a Turance.

A ƙarƙashin tsarin, kamfanoni da kuma ɗaiɗaikun mutane kan yi rajista da bankin da suke so, inda za a dinga ba su garin kuɗin fiye da yadda masu game-garin asusu za su samu.

Saboda haka duk lokacin da ‘yan POS suka fuskanci ƙarancin takardun kuɗin a sassan Najeriya hakan na nufin ƙarancinsu a hannun jama’a.

“Bankunan kasuwanci kan bai wa masu kamfani 500,000 a kowace rana, amma yanzu abin da suke samu bai wuce 50,000,” kamar yadda Ibrahim Abdullahi, wani ɗan POS a Abuja, ya shaida wa BBC Hausa.

Ya ƙara da cewa masu POS ɗin da ba na kamfani ba kuma kan samu kamar 100,000 a rana. Amma shi Ibrahim ya yi rajista ne a matsayin kamfani.

“Kamar yau da na tura banki ba a samu sama da 50,000 ba. Labarin da muke samu ma na cewa waɗanda ba na kamfani ba su samun fiye da 10,000 ko 20,000,” a cewarsa.

Me ke jawo ƙarancin takardun naira?

Akasarin masu ruwa da tsaki a harkar hada-hadar kuɗi kan ɗora alhakin kan dalilai da dama, amma dukkansu sun yarda cewa CBN, da bankunan kasuwanci, da ‘yan kasuwa ne jawo matsalar.

Kazalika, sun ce har yanzu sauya kuɗin da aka yi a 2022 na bibiyar hada-hadar kuɗi a faɗin ƙasar, duk da cewa CBN ya tabbatar cewa za a ci gaba da amfani da tsofaffi da sababbi.

Ƙungiyar ma’aikatan bankuna a Najewriya ta ce ba ta da wasu cikakkun bayanai game daga hukumomi game da dalilin da ke jawo ƙarancin kuɗin.

Sai dai wani babban jami’in ƙungiyar ya faɗa wa BBC Hausa cewa “alamu sun nuna CBN na son ƙaƙaba wa ‘yan Najeriya tsarin kasuwanci ba tare da garin kuɗi ba [cashless] ko da cigabanmu ya kai ko bai kai ba”.

Shugaban ƙungiyar masu POS a Najeriya ta Association of Mobile Money Operators of Nigeria (Ammon), Salihu A. Umar, ya ce matsalar ta fi ƙamari a jihohin Kano da Abuja.

“Waɗansu mutane ne suka fara riƙe kuɗaɗen a hannunsu, saboda suna cewa bankunan sun fara riƙe kuɗaɗen, su kuma suna da buƙataun da suke son yi a hannun su,” a cewar Salihu Umar.

Shi ma wani ɗan POS a birnin Kano mai suna Shu’aibu Abdullahi ya goyi bayan wannan dalili yana mai cewa akwai ‘yan kasuwar da suke da kwastomomi ‘yan POS, waɗanda suke bai wa kuɗaɗen idan sun yi ciniki maimakon banki.

“Ba kowa ne ke ɗaukar kudin ya kai banki ba, wani ma zai ce maka yana da kwastoman POS da yake bai wa garin kuɗin nasa baki ɗaya a kullum,” in ji shi.

Salihu Umar ya ƙara da cewa da yawan masu POS ɗin kan bi gidajen mai, da kasuwanni don neman garin kuɗin, maimakon bankuna.

Tsarin kasuwanci ba da garin kuɗi ba (cahsless) – Ƙilu ta ja bau

A watan Oktoban 2022 ne CBN ya sanar da sauya fasalin kuɗi na naira 200, da 500, da kuma 1000, kuma ya buƙaci masu kuɗi a hannu su mayar da su bankuna cikin ƙasa da kwana 50.

Bankin ya ce idan mutane suka mayar da kuɗaɗen ba tare da ɓata lokaci ba za su iya samun musayar kuɗinsu a kan kari.

Haka nan sabon tsarin ya sa an cire duk wani caji da ake yi a kan kudin da ake kai wa bankuna duk yawansu da zimmar ƙarfafa wa mutane gwiwar mayard a kuɗin.

A lokacin, CBN ya ce sama da kashi 80 na kuɗin da ke yawo tsakanin ‘yan Najeriya ba ya shiga bankuna.

Wani babban ma’aikacin banki a Najeriya da ya nemi a sakaya sunansa ya faɗa wa BBC cewa ƙarancin takardun kuɗin na da alaƙa da kuɗaɗen da CBN ya karɓe daga hannun mutane ta hanyar bankunan kasuwanci lokacin da ya sauya fasalin naira.

“Abin da ya bai wa bankuna da ‘yan kasuwa mamaki shi ne, ko kashi 10 cikin 100 na kuɗin da aka karɓe, triliyan biyu da ɗoriya, ba a sake mayar da su banki ba,” in ji shi.

“Ma’ana tun da mutane suka sake karɓar kuɗaɗensu daga bankuna ba su sake mayar da su banki ba.”

Babu wasu alƙaluma da ke nuna yawan kuɗin da CBN ke karɓa daga hukumar buga kuɗaɗe ta Najeriya tun daga lokacin da aka sauya fasalin kuɗin.

Saboda a ƙaranta yawan kuɗin da ke yawo a hannun mutane, CBN ya ƙayyade adadin kuɗin da mutum zai iya cirewa a mako zuwa N5,000,000 ga mutum ɗaya, yayin da kamfanoni za su iya cire N5,000,000.

Bugu da ƙari, N20,000 kacal mutum zai iya cirewa daga na’urar ATM a kullum. Su kuma bankunan kasuwanci sun sake ƙayyade yadda mutum zai iya cire kuɗin ta yadda ba za a cirar sama da N5,000 ba a lokaci guda, kodayeke daga baya wasu bankunan sun ɗan ƙara.

Babban jami’in ya ce bankunan kasuwanci sun sake karɓar kuɗaɗen daga CBN waɗanda suka kai kusan tiriliyan biyu da 700,000 bayan babban zaɓe na 2023.

“Da ma su bankuna ai karɓar kuɗi suke yi su ajiye saboda idan mai nema ya zo su ba shi, shi ya sa kuɗin ke jujjuyawa a hannun mutane.

“Amma yanzu bayanan da muke samu shi ne babu tsofaffin kuɗin masu yawa a hannun CBN, sai dai sababbi.”

Laifin bankuna ne da kwastominsu – CBN

A watan Nuwamban da ya gabata ne Babban Bankin Najeriya ya amince cewa akwai yiwuwar aukuwar ƙarancin takardun kuɗin a tsakanin ‘yan ƙasa a wasu manyan birane.

A martanin da ya mayar, bankin ya ce yana da isassun kuɗi a lalitarsa, amma kuma ya ɗora alhakin ƙaranci kuɗin kan bankunan kasuwanci da kwastomominsu.

“Binciken da muka yi ya nuna cewa an samu ƙarancin ne saboda cirar kuɗaɗe masu yawa daga rassan CBN da bankunan ajiya ke yi, da kuma rububin cirar kuɗin da wasu kwastomomi ke yi daga ATM,” in ji sanarwar da ya fitar ranar 2 ga watan Nuwamba.

Bankin ya nemi nemi ‘yan ƙasa su kwantar da hankalinsu, yayin da “rassan CBN ke ƙara ƙoƙarin yaɗa kuɗaɗen a jihohin da suke”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here