Home Tsaro Me kaddamar da dakarun sa-kai da jihohin arewacin Najeriya ke yi ke...

Me kaddamar da dakarun sa-kai da jihohin arewacin Najeriya ke yi ke nufi?

150
0
Tsaro a arewa 2

Jihar Zamfara ta kasance ta biyu a jerin jihohin da suka kaddamar da rundunar jami’an tsaron sa-kai a hukumance, bayan jihar Katsina da ta kaddamar a bara.

Hakan dai ba ya rasa nasaba da irin kamari da matsalar tsaro ke kara yi a yankin arewa maso yammaci da ma fadin kasar baki daya.

Jihar Zamfarar dai ta kaddamar da rundunar tsaron ta sa-kai mai suna “Askarawan Zamfara” mai dakaru guda 2,646 daga kananan hukumomi 14 na jihar.

Gwamna Dauda Dare ya ce “dakarun sun samu horo na musamman daga jami’an tsaro da kwararru daban-daban a fannin tsaro don tunkarar matsalar `yan bindiga masu satar mutane da dabbobi a jihar Zamfara”.

Gwamnan ya kuma yi nuni da cewa sauran jihohin arewacin Najeriya su ma za su kaddamar da irin wadannan jami’an tsaron na sa-kai domin yi wa ‘yan bindigar kofar rago.

Da ma dai jihohin arewa maso gabas sun kaddamar da ‘Civilian JTF’ domin yakar Boko Haram sannan jihohin kudu maso yammaci suna da “Amotekun” inda su kuma jihohin kudu maso gabas suke da “Ebebuagu”

Me hakan yake nufi ga sha’anin tsaro a Najeriya?

Tsaro a arewa 1

Masana tsaro a Najeriya da ketare na ta tofa albarkacin bakinsu kan kaddamar da zaratan matasan domin tunkarar ‘yan bindiga da jihohin yankin arewacin Najeriya ke fama da shi.

Malam Kabiru Adamu shugaban kamfanin tsaro na Beacon Consulting da ke Abuja Najeriya ya ce wannan yana nuni da irin gazawar tsarin tsaro na gwamnatin tarayyar Najeriyar, inda ta bar al’amarin sakaka a hannun jihohi.

“Kafa rundunar tsaro ba mafita ba ce, ya kamata Majalisar kasa ta sauya kundin tsarin mulki domin samar da ‘yan sandan jihohi cikin tsari ta hanyar ba su cikakken horo da sauransu”, in ji Malam Kabiru.

To sai dai Barrister Bualama Bukarti wanda masanin tsaro ne kuma lauya mai zaman kansa a Burtaniya ya ce “duk da cewa bai zama lallai wannan tsari ya zama shi ne mafita ba, amma ba za ka soki jihohin ba saboda duk wanda ruwa ya ci, to ko takobi ka mika masa zai kama ne.”

Mene ne illar tsarin ko alfanunsa?

Malam Kabiru Adamu ya ce abin da jihohin Zamfara da Katsina suka kusan dukkan jihohin Najeriya na da irin tsarin ko da kuwa ba a hukumance ba.

Tsaro a arewa 3

“Akwai mutum 40,000 da jihohi 14 na Najeriya suka dauka irin wannan aiki sannan babu wata karamar hukuma a 774 na Najeriya da za ka je ba tare da irin wadannan rundunoni na taimakon yankunansu ba”, in ji Malam Kabiru.

Masanan guda biyu sun kara da cewa idan dai dai har gwamnatin tarayya ba za ta nemi majalisar dokoki ta yi doka kan irin wannan tsari, to shirin na da kalubale babba.

“Tunda dai da alama gwamnati ta gaza, to dole ne a yi doka domin tsaftace tsarin yadda ba za a bar abin kara zube ba.” In ji Barrister Bulama Bukarti.

Masanan sun kuma lissafa wasu matsaloli na tsarin daukar matasa aikin sa-kai kamar haka:

  • Za a iya samun yawaitar makamai a hannun ‘yan kasa wanda hakan zai haifar da karin matsalar tsaro a nan gaba.
  • Karancin horo ga mai rike da makamai da ka iya haifar da wuce gona da iri.
  • Rashin cikakkun bayanai dangane da mutanen da aka diba, inda wasu ma ba su da halayya mai kyau.
  • Daukar hukunci a hannunsu musamman ma cin zarafin wanda ba su ji ba ba su gani.

Mece ce mafita?

Malam Kabiru Adamu da Barrister Bulama Bukarti sun amince cewa kafa rundunar tsaro ba mafita ba ce ga jihohin da ke fama da matsalar.

To sai dai sun amince cewa a rashin uwa a kan yi uwar daki, inda suka ce ya kamata Majalisar kasa ta sauya kundin tsarin mulki domin samar da ‘yan sandan jihohi.

A cewarsu ‘yan sandan jihohi za su fi zama cikin tsari da samun cikakken horo kasancewar doka ce ta kafa su.

To amma masanan sun ce idan ba a iya samun dokokin ba to sai a bi wasu shawarwari da suka bayar kamar haka:

  • Gwamnatin tarayya ta fito da tsarin yadda za a rinka kafa irin wadannan kungiyoyi a jihohi na bai daya.
  • Tabbatar da cewa wadannan matasa za su yi aiki ne kadai yayin da suke cikin rakiyar jami’an tsaro domin gudun arangama.
  • Lallai a tanadi rumbun tattara bayanan matasan da irin horon da aka ba su da kuma makaman da aka ba su, kuma za a cimma hakan ne a karkashin ma’aikatar tsaro ko kuma ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here