Home Uncategorized Matsin Tattalin Arzikia: Talakawa Ku Taya Mu Da Addu’a Wajen Lalubo...

Matsin Tattalin Arzikia: Talakawa Ku Taya Mu Da Addu’a Wajen Lalubo Mafita – Hon. Leko, Dr. Gwalabe

149
0
IMG 20240501 WA0095

An nemi addu’ar Yan Najeriya a wani mataki da zai tallafawa yunkurin Majalisar Wakilai na samar da kudure- kudure da za su inganta rayuwar su ta fannin tattalin arziki da Cigaban Kasa.

Dan Majalisar Taraiya mai Wakiltar mazabar Bagoro da Dass da ga Jihar Bauchi, Hon. Jafaru Gambo Leko ne ya gabatar da wannan bukatar a wurin taron karawa juna sani na wuni 2 da Majalisar ta shirya don zaburar mambobin ta akan aiyukan da su ka saka a gaba a Abuja.
Ya ce Shugabanci batu ne mai girma ko da na iyalin ka ne sabo da haka ne Majalisar ta shirya wannan taro don ya tallafawa mambobin ta da Sabbin dabaru na yin dokokin da za su inganta rayuwar Yan Najeriya.
Hon. Leko ya ce taron an shirya shine akan batutuwa guda uku da su ka hada da inganta tattalin arziki da fannin man fetur da kuma Sabbin dabarun Tara haraji. In da ya ce duk wadannan su na da alaka da rayuwar Yan Najeriya.
Dan Majalisar ya ce musamman batum man fetur ya na da alaka da rayuwar Yan Najeriya baki daya ganin yadda cire tallafin Man ya shafi rayuwar su baki daya da kuma halin da ake ciki na karancin sa a halin yanzu.
Leko ya ce Majalisar ta gaiyaci kwararru domin su bayar da shawarwari da za su tallafawa Yan Majalistaar wajen yin dokokin da za su inganta rayuwar Yan Najeriya.
Ya yabawa yunkurin Majalisar Wakilai na shirya wannan bita a lokacin da ya dace musamman ganin sun  dawo da ga hutu don fuskantar aiyukan da su ke gaban su.
Hon.  Dr. Auwalu Abdu Gwalabe da ke Wakiltar mazabar Katagun da ga Jihar Bauchi Dan jam’iyyar PDP ya yabawa yunkurin Majalisar na shirya taron karawa juna sani don lalubo Sabbin dabarun da za su fidda Yan Najeriya daga matsin tattalin arziki da su ke ciki.
Ya cre a matsayin su na Yan Majalisar Taraiya Wakilan jama’a sun damu mutuka da halin da Yan Najeriya su ke ciki sabo da haka ne aka shirya wmannan taro don nemam mafita ko Yan Najeriya sa samu sauki.
Hon. Gwalabe ya kara da cewa bayan batum tattalin arziki akwai matsalar tsaro da ta addabi kasarnan wadda ita ma ta taimaka wajen matsalar tattalin arziki inda ya ce Majalisar ta himmatu wajen shawo kan matsalar.
Dan Majalisar ya nemi hadin kan Yan Najeriya wajen hada karfi da karfe don magance matsalolin da suka addabi kasarnan

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here