Home Mulki Matsi Na Tattalin Arziki: Ya Zama Wajibi Gwamnatin Tinubu Ta Gaggauta Lalubo...

Matsi Na Tattalin Arziki: Ya Zama Wajibi Gwamnatin Tinubu Ta Gaggauta Lalubo Mafita – Inji Hon. Fulata

108
0
Hon. Fulata a

Dan Majalisar Wakilai Abubakar Fulata ya ja Hankalin Gwamnatin  Bola Ahmad Tinubu da ta gaggauta lalubu mafita na halin da Yan Najeriya suke ciki na matsi na tattalin arzikin  kasa domin rayuwa ta yi tsanani kafin mutane su fita da hanyacin su.

Hon. Fulata wanda ke Wakiltar Birniwa da Guri, da Kirikasamma da ga Jihar Jigawa ya yi wannan jan hankali ne yau Talata a ofishin sa bayan da Majalisar Taraiya ta gana da Ministocin Kudi da na Kasafin Kudi da Tsare-tsare da Gwamnan Babban Banki Kasa (CBN) da kuma Shugaban Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS).

Fulata ya ce Majalisar ta gaiyace su ne domin ta yi binci ke akan me Gwamnatin ta ke yi domin lalubo mafita ga Yan Najeriya na matsi na tattalin arziki da tsadar rayuwa da suke ciki.

Ya ce sun yi mu su tambayoyi ma su tarun yawa na matakai da tsare-tsare da gwamnati take dauka na warware matsalolin da ake ciki amma sun amsa kadan da ga ciki tambayoyi da su ka yi mu su, a ya yin da basu amma mafi yawa da ga tambayoyin da su ka yi mu su ba.

Hon. Fulata ya ce koda yake za a iya yi mu su uzuri na samun kasar da su ka yi da matsaloli da dama amma ya zama wajibi su hanzarta lalubo bakin zaren domin Yan Najeriya su na cikin  wani hali na tsadar rayuwa da tashin gwauron zabi da kayan masarufi su ke yi.

Shi ma Hon. Sada Soli Danmajalisar Taraiya da ke Wakiltar Jibiya da Kaita da ga Jihar Katsina ya tabbar da  halin da Yan Najeriya su ke ciki in da ya ce ya na kyakkyawan zato da kwarin gwiwa cewa matakai da Gwamnatin ta ke dauka za su haifar da da mai ido.

Hon. Soli

Hon. Soli ya kara da cewa da ga bayanan Ministocin da sauran shugabannin Hukumomin da su ka gayyata matakai da gwamnati ta ke dauka ta fannonin hana tashin gwauron zabi da Dala ta ke yi da tashin farashin kayayyakin abinci da yardar Alllah za su za mo tarihi a kasarnan.

Da ga karshe ya bawa Yan Najeriya hakuri na halin da su ka sami kan su a ciki tare  da yi mu su albishir cewa matakai da gwamnati ta ke dauka za su kawo sauki a kasa baki daya nan da dan wani lokaci mai zuwa.

Tun da farko Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsare Atiku Bagudu ya ce hakkin Majalisar Taraiya ne da Yan Najeriya da su ji bahasi da ga Gwamnati na irin nauyi da aka dora mu su na yadda su ke tafiyar da al’amura.

Ya ce sun zo kuma sun amsa tambayoyi da Yan Majalisar Wakilai su ka yi mu su akan tsare-tsare da matakai da Gwamnatin Taraiya ta ke dauka na samawa Yan Najeriya sauki na halin matsi na tattalin arziki da ake ciki da tashin farashin kayan masarufi da Dalar Amurka.

Game da matakai da Gwamnati ta ke dauka game da tashin hauhawar farashi da ake samu na kayan masarufi , Bagudu ya ce babbar mafita it ace a karfafawa Yan kasa da tallafi domin su samar da kayayyaki da ake bukata a cikin Kasa da wadan da za a rinka fitar da su kasashen waje; wanda ya ce ita ce babbar hanya ta karfafa darajar Naira.

In da ya ce Gwamnatin Tinubu ta na da tsare-tsare na tallafawa Yan Kasa ta fannin Noma da tono ma’adanai da sarrafa su da sauran hanyoyi da za su kawo sauki ga Yan Najeriya da ma Kasa baki daya.

Har ila yau, game da bashi da ake ciyowa ya ce ba laifi bane ciyo bashi amma abu mafi a’ala shi ne idan an ciyo bashin me za a yi da shi. Idan abun da zai kawo cigaba ne da bunkasa tattalin arzikin Kasa ba matsala bane domin kowacce kasa a duniya ta na cin bashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here