Home Tsaro Matsalar Tsaro: AN Shawarci Gwamnonin Arewa Da Su Zamo Tsintsiya Madaurin Ki...

Matsalar Tsaro: AN Shawarci Gwamnonin Arewa Da Su Zamo Tsintsiya Madaurin Ki Daya

131
0
Sanata Dandutse

An shawarci Gwamnonin Arewa da sauran shugabannin al’umma da su kasance tsintsiya madaurinki da ya wajen tunkarar matsalar tsaro da ta addabi yankin  Arewa shekara da shekaru a wani mataki na kawo karshen matsalar baki da ya.

Wannan shawara ta fito ne da ga bakin dan Majalisar Taraiya mai Wakiltar Katsina ta Kudu, Sanata Dandutse Muntari Muhammed a yayin da ya ke ganawa da Yanjaridu a ofishin sa da ke Majalisar Dattawa a birnin Taraiya Abuja a yau Juma’a.

Ya ce matsalar tsaro da ta addabi yankin Arewa zata zo karshe ne kawai idan an hada karfi da karfe wuri guda wato Gwamnonin Arewa da sarakuna da Dakatai da masu Unguwanni  da Malaman addina da kungiyoyin al’uma sun amince su kawo karshen wannan matsala.

Sanata Dandutse ya kara da cewa Gwamnoni ya zama wajibi su dunkule wuri guda, kowannen su ya yi koyi da Gwamnan Jihar Katsina Dikko radda ta hanyar kafa kungiyoyi tare da neman dukkannin masu ruwa da tsaki wajen yakar matsalar tsaro da ta addabi yankin Arewa.

Ya ci gaba da cewa idan ba a hada kai ba toh, zai yi wuya a kawo karshen matsalar sabo da idan Gwamnoni su na yi dai dai ku to zai zama ne, a na tubka ana warwarewa. In da ya bada misali da cewa idan Gwamatin Katsina ta na yakar yan ta’adda za su gudu ne su koma Jihar Zamfara ko Kaduna ko Niger. Sabo da haka ya zama wajibi a hada kai idan ana so a kawo karshen matsalar.

Bayan haka ya ce dukkanin ma su marawa yan ta’adda baya su ma ya zama wajibi a yake su ta hanyar hukunta duk wanda aka samu yana bayar da bayanai da masu sayen shanun da su ka sato da sauran kayayyaki da su ke kwacewa a hannun al’umma.

Har ila yau, Sanata Dandutse ya bayar da shawarar cewa matasan Arewa ya zama wajibi su farka da ga barcin da su ke yi. Su ta shi su nemi na kansu, su daina raina karamar sana’a domin da ga karama ta ke komawa babba; in da ya bayar da misali da wani mai karamar sana’a wanda ya gina gida da ga jari da aka ba shi na naira dubu goma kacal.

Ya ja hankalin samarin Arewa da su rinka yin duba ga takwarorin su na Yankin Kudu da ma wasu kasashe da suke jajircewa wajen nema wanda hakan ya kawar musu da zaman banza ku ma ya samar musu sana’a abar dogara wacce ta bunkasa tattalin arzikin su.

Da ga karshe Sanata Dandutse ya shawarci shugabanni a dukkan mataki da matasa da su ji tsoron Allah; su sani cewa duk abun da suka aikata Allah zai tuhume su akan sa ranar gobe kiyama. In da ya kara da cewa ba bu makawa kowa sai ya fuskanci hukunci a wurin Allah na abun da ya aikata mai kyau ko aka sin sa. Sabo da haka ya hore su da su yi hattara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here