Home Siyasa Masu yi wa ƙasa hidima ne za su yi aiki da na’urar...

Masu yi wa ƙasa hidima ne za su yi aiki da na’urar BVAS ranar Zaɓe – INEC

201
0

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya ta ce Masu yi wa ƙasa hidima ne kadai za su yi amfani da na’aurar tantance masu kaɗa ƙuri’a ta BVAS a ranar zaɓe.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci cibiyoyin da ake bayar da horo ga ma’aikatan wucin-gadi da hukumar ta ɗauka dan gudanar da aikin zaɓen, a Abuja babban birnin ƙasar.

Farfesa Yakubu ya ce domin samun nasarar gudanar da zaɓen hukumar na buƙatar haɗin kan masu yi wa ƙasa hidima.

Haka kuma shugaban hukumar ya yi kira ga masu yi wa ƙasa hidimar da su zama masu biyayya ga Najeriya da ‘yan Najeriya ba jam’iyya ko wani ɗan takara ba.

Ya sake jajjada musu cewa kada su yadda su bayar da na’uara BVAS ɗin ga wani jami’in zaɓen, yana mai cewa za a riƙa bibiyar kowane ɗaya daga cikinsu.

Yakubu ya ce “Najeriya ta yi sa’a da ta samu ‘yan ƙasa irinku. Babu yadda za a yi INEC ta gudanar da zaɓe ba tare da masu yi wa ƙasa hidima ba. Kun zama dole sai da ku ake gudanar da zaɓen Najeriya. ba za mu iya gudanar da zaɓe ba tare da taimakonku ba.”

“Dan haka mun dogara a gareku da sauran ma’aikata.Kuma ku ne za ku yi amfani da abu mafi muhimmanci (BVAS) a harkar gudanar da zaɓen a kowacce rumfar zaɓe, inda kowanne mutum zai je domin kaɗa ƙuri’arsa. saboda haka kowanne daga cikinku zai rantse cewa zai zama ɗan ba-ruwanmu a zaɓen. Za ku yi biyayya ne ga Najeriya ba wata jam’iyya ko ɗan takara ba. Ku ne wakilan INEC a rumfunan zaɓen. Dan haka ku ne sarakai a rumfunan zaɓ”. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here