Home Uncategorized Masu Su Ka Na Akan Sayen Tukwane Da Likkafani Su Na Yi...

Masu Su Ka Na Akan Sayen Tukwane Da Likkafani Su Na Yi Ne A Bisa Jahilci Ko Kiyayya – Sanata Hanga

153
0
Sen. Hanga 2

Sanata Rufa’I Sani Hanga ya ce wadanda su ke sukan sa akan tallafin da ya bayar na tukwane da likkafani suna yi ne a bisa dalili na jahilci ko kiyayya amma hakan bai dame shi ba domin abun da yake yi yana yi ne don Allah da tallafawa talakawa masu karamin karfi da ke mazabar sa.

Sanatan ya mayar da wannan martanine jiya Talata a hirar sa da Yan jaridu a ofishinsa da ke birinin Taraiya Abuja.

Sanata Hanga ya ce aiyukan da ya ke yi bashi ya ke yin su da ga aljihun sa, ba aiyuka ne na Kwansituwansi ba kamar yadda wasu mutane su ke fada. In da ya ce a har ya zuwa yanzu ba a saki kudaden Kwansituwansi da ake bawa Yan Majalisar Taraiya ba.

“ina yin aiyuka ne don Allah, domin shi ne rabo na kuma dan taba rayuwar talakawa kai tsaye. Domin tukwanennan da ake Magana akan su, zaka ga sauda yawa za anyi mutuwa amma a rasa tukunyar da za’a bunne mutum sai an nemo. Ko kuma an rasa likkafani. Sabo da haka na samar da wadannan abubuwa ne domin da zarar an bukata ce, akwai su a kasa, ba sai anje neman su ba, musamman ga talakawa da ba su da hali”.

Hanga ya kara da cewa mutane su na so ne su rinka maganganu akan abubuwa kawai amma akwai aikace-aikace da ya yi masu yawa amma ba su mutane su ke so su yi magana akan su ba.

In da Sanata Hanga ya ce ya gina makarantun Islamiyya guda 2 kuma ya sayi fili  domin a gina wata makarantar. Ya ce ya tallafawa mata 2000 da jari na naira dubu 50 kowannnen su domin su yi sana’a daban-daban.

Bayan haka, Sanata Hanga ya ce ya biyawa matasa mutum 200 wadanda su ka kasa biyan kudin rijista a jami’o’I sakamakon Karin kudin makaranta da aka yi wandanda dukkannin su ba za su iya biya ba wanda hakan na nufin za’a kure su a makarantar idan ba su biya ba.

Har ila yau, Sanata Hanga ya ce ya biyawa matasa mutum 250 da su ke Politeknik kudin makaranta, da kuma mutum 1,112 wadanda ya biyawa kudin jarabawa na JAMB a wani mataki na tallafawa yayan talakawa masu karamin karfi domin ya ingata rayuwar su.

Ya ce duk wadannan aiyuka da ya yi mutane ba su gani ba, sai Tukwane da Likkafani da ya saya ake cece-kuce akan su. Wadanda su ma ya saye su ne domin tallafawa talakawa da ba su da hali musamman a lokacin da su ka rasa yan uwan su.

Sanata Rufa’I Hanga ya ce ya na alfahari da abun da ya yi na sayen Tukwane da Likkafani domin aiki ne da ya ke yi na tallafawa talakawa masu karamin karfi a lokacin da su ke da bukatar taimako na gaggawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here