Home Kwadago Masu Ruwa Da Tsaki Kan Shari’a Sun Nemi Karin Albashi Sama Da...

Masu Ruwa Da Tsaki Kan Shari’a Sun Nemi Karin Albashi Sama Da Kaso 300

134
0
IMG 20230811 WA0108

Masu ruwa da tsaki akan harkar Sharia sun nemi da a kara albashin ma’aikatan Sharia da sama da ka shi 300 da ga abin da Shugaban kasa da Majalisar Taraiya su ka gabatar.

 

Sun nemi wannan kari ne a wurin taron jin ra’ayin jama’a da Majalisar Dattawa ta shirya akan Kudurin Doka da aka gabatar wanda ya ke neman a kara albashin Ma’aikatan sharia musamman manyan Joji-joji na Kotunan Kasarnan da ya gudana a jiya Litinin a zauren Taron Majalisar Dattawa.

 

Su ka ce karin ya zama wajibi lura da tsananin rayuwa sakamakon cire tallafin Man fetur da hauhawar farashin kayan masarufi a kasarnan.

 

A yayin da ma’aikatan Sharia su ke bukatar Karin albashi ita kuma Hukumar da take da alhakin kara albashi ta Kasa wato RMAFC ta nemi Majalisar da ta amince da Karin da ta gabatar wanda ta ce tayi la’akari ne da Doka mai lamba 84 da kuddin Tsarin Mulkin Najeriya na shekara ta 1999 da aka gyara ya ce.

 

Sai dai Shugaban Kwamitin Sharia na Majalisar Datttawa, Sanata Tahir Munguno cewa ya yi ya lura cewa akwai rudani game da bukatar da Hukumar RMAFC ta gabatar domin taci karo da umarnin Shugaban Kasa da Majalisar Taraiya.

 

Sabo da haka Shugaban ya bukaci Hukumar RMAFC da Shugabannin Kwamintin Shari’ar na Majalisar da su zauna don su fahimci umarnin  na Shugaban Kasa da kuma amincewar da Majalisar Taraiya ta yi don kaucewa yin kuskure.

 

Wannan bukata ta yin Karin albashi ga Shugiaban Kasa da Mataimakin sa da  Gwamnoni da Mataimakan su da           Ministoci da masu bawa Shugaban Kasa shawara da Yan Majalisar Taraiya an gabatar da ita ne tun shekara ta 2022, wanda akan haka ne aka gabatar da Kuduri na Doka domin ya bayar da ikon yin hakan.

 

Kudurin ya samu amincewar Majalisar Taraiya wanda a halin yanzu ya kai zangon jin ra’ayin jama’a akan Dokar. Wanda a halin yanzu bayanai da ak tattara a wurin jin ra’ayin jama’a shine Kwamitin zai yi amfani da shi wajen gabatar da rahoton sa  ga zauren Majalisar Taraiya.

 

Abun da ya rage shine Kwamitin zai gabatar da rahoton sa nan da yan kwanaki masu zuwa wadda ita kuma Majalisar Taraiya za ta yi duba akan rahoton sannan ta yanke hukunci.

 

Da zarar ta amince da wannan kari na albashi, Majalisar Taraiyar zata gabatar da Dokar ga Shugaban Kasa wadda da zarar ya rattaba hannu kan Karin Albashin, ya zama Doka.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here