Home Siyasa Manyan jam’iyyun Najeriya sun bayyana matsayarsu kan shawarar Atiku

Manyan jam’iyyun Najeriya sun bayyana matsayarsu kan shawarar Atiku

199
0
Yan Takarar Shugaban Kasa

Manyan jam’iyyun Najeriya sun bayyana mabambantan ra’ayoyinsu game da shawarwarin da tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya ƙarƙashin jam’iyyar PDP Atiku Abubuakar ya bayar.

Atiku Abubakar ya bayar da shawara kan tursasawa hukumar zaben Najeriya INEC amfani da naurar zaɓe da kuma daura sakamako a Internet kafin sanar da wanda ya samu nasara.

Ya ce kamata ya yi a riƙa yanke hukuncin shari’un zaɓe gabanin rantsar da wanda aka ayyana ya ci zaɓe idan akwai kalubalantar da yake fuskanta ta shari’a.

A ganinsa kamata ya yi a mayar da mulkin shugaban ƙasar zango daya na shekara shidda kawai, maimakon zango biyu na shekaru hudu-hudu, da kuma yin karɓa-karɓa tsakanin shiyyoyi shidda da ke kasar, domin damawa da kowanne ɓangare.

Waɗannan shawarwari sun samu goyon baya daga jam’iyyarsa ta PDP inda Malam Ibrahim Abdullahi mataimakin sakataren watsa labarai na jam’iyyar ya ce abin da Atiku ya nema bai saɓa ka’ida ba.

“Atiku na nufin tunanin da shugabannin ke da shi na cewa duk wanda ya ci mulki karin farko sai ya dawo karo na biyu ya kau, saboda duk abin da mutum ba zai iya aiwatarwa ba a shekara shida hakan na nufin ko takwas ka ba shi ba zai iya yin komi ba.”

An tambayi Malam Ibrahim cewa da a ce Atiku ne ya ci mulki zai iya bayar da wannan shawara sai ya ce “rashin cin zaɓensa ba ya nufin ba zai bayar da shawara ba, ko ko rashin cin zaɓensa na nufin ba shi da sauran ‘yanci a matsayinsa na ɗan Najeriya?.”

To ko yaya jam’iyyar APC mai mulki ta kalli wadannan shawarwari da Atikun ya bayar ?.

Malam Bala Ibrahim, shi ne daraktan watsa labarai na jam’iyyar ta APC, ya ce idan da zuciya ɗaya Atiku ya bayar da waɗannan shawarwari to ya yi abin a yaba.

“Abin tambaya zafin kayi ne yasa yake wannan magana ko kuma a a ya yi ne da zuciya guda. Idan zafin kayi ne domin kowa ya rasa babu wanda zai kalli wannan shawara ballantana a yi aiki da ita.

“Da kuma da gaske Atiku yake da kamata ya yi ya bayar da wannan shawara kafin a yi zaɓe, amma yanzu an kayar da shi ya zo da wannan batu, abin a mayar masa ne,” in ji Bala Ibrahim na APC.

BBC ta tuntuɓi jam’iyyar Labour wato LP domin jin nata ra’ayin game da wannan shawara ta Atiku wadda ta ce akwai abun dubawa a ciki.

Dr Tanko Yunusa, shi ne kakakin jam’iyyar na kasa ya ce sun amince da shwarar mayar da mulki shekara shida falle daya.

“Ai da haka za a kaucewa irin wannan abin da muke gani a yanzu, mutum guda ya mamaye ɓangaren shiri’ar ƙasarmu, kuma sai ya koma karo na biyu idan ba a ɗauki mataki ba.”

A Najeriya dai na jima ana ba da shawarar yin gyara ga kundin tsarin mulkin kasar domin inganta harkokin zabe.

Mataki na baya-bayan nan shi ne amincewa da sabuwar dokar zaben kasar gabanin zabukan 2023 da aka yi.

‘Babu wani abu sabo a kalaman Atiku’

Baya ga jam’iyyun siyasa masu sharhi ma sun fara tofa albarkacin bakinsu kan waɗannan kamalai na Atiku.

Dr Abubakar Kari Malami ne a jami’ar Abuja kuma mai sharhi kan al’amuran siyasa a Najeriya, ya ce ‘babu wani abu sabo a kalaman Atiku Abubakar’.

Ya ce mutane da dama za su kalli kalaman Atiku a matsayin fargar daji, saboda za su yi tsammanin ya bayyana hakan ne saboda ya faɗi zaɓe, ya kuma je kotu bai samu nasara ba.

Da yawan al’umma ba za su yarda cewa ya yi hakan ne da zuciya ɗaya ba.

Da dama daga cikin abubuwan da faɗa akwai su a ƙasa, wasu ma na daga cikin shawarwarin da kwamitin da gwamnati ta kafa na lokacin Lawal Uwais da aka kafa a 2007/08.

“Maganar karɓa-karɓa ba za ta yi wa mutanen arewa kyau ba. Kuma tun asali ba ta cikin tsarin mulki, domin tsarin mulkin ƙasar nan shiyya biyu ya sani daga Kudu sai Arewa.

“Idan har ana so a yi hakan, ai ba sai an sanya shi cikin kundin tsarin mulki ba, sai a bai wa jam’iyyun siyasa dama su yi hakan da kansu.

” A baya NPN ta yi haka, jam’iyyar PDP ta yi haka, kai har ma ita APC mai mulki duka sun yi,” in ji Dr Kari.

Game da shawarar shekaru shida kuwa da Atiku ya yi magana, Dr Kari ya ce ba wani sabon abu ba ne hakan, “tun lokacin Obasanjo ya so a yi hakan bai yi nasara ba,”.

Amma a ra’ayin Dr Kari shekara shida falle guda za ta rage zaƙewa da dagewa kan sai mutum ya koma kan mulki. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here