Home Uncategorized Majalisar Wakilai Ta Yi Alkawarin Hada Gwiwa Da Hukumar Almajiri Don Ganin...

Majalisar Wakilai Ta Yi Alkawarin Hada Gwiwa Da Hukumar Almajiri Don Ganin Yara Sama Da Miliyan 10 Suna Zuwa Makaranta

109
0
Almajiri Nass Visit

Majalisar Wakilai ta sha alwashin ganin ta hada gwiwa da Hukumar Almaji da sauran Hukumomi don ganin ta mayar da yara sama da miliyan 10 da ba sa zuwa makaranta sun koma don samar mu su da ilimi na zamani da na addini da zai tallafa wajen kawo cigaba mai dorewa a kasarnan.

Shugaban Kwamitin Ilimi na Musamman na Majalisar Wakilai, Hon. Almustapha Aliyu dan jam’iyar APC da ga Jihar Sokoto ne ya fadi haka a lokacin da Shugaban Hukumar Almajiri da Wadanda ba sa Zuwa Makaranta ya kai ma sa ziyara a ofishin sa da ke Majalisar Wakilai jiya Alhamis.

Hon. Almustapha ya ce burin Majalisar Wakilai shine ta ga yara da ba sa zuwa makaranta da Almajirai sun sami ilimi mai inganci wanda zai taimaka wajen gina kasarnan a maimakon zaman banza wanda shi ke haifar da fituntunu da su ka addabi kasarnan kamar su sace-sace da ma ta’addanci.

Dan Majalisar ya ce tsarin da su ka fito da shi wanda su ka yi wa lakabi da NiMPROP tsari ne na shekara hudu wanda burin sa shine ya ga ya mayar da yaran da ba sa zuwa makaranta, makaranta don rage yawan su a Najeriya.

Ya ce shiri ne na hadin gwiwa tsakanin Hukumomin Gwamnati da Kungiyoyi na cikin gida dama na wajen kasarnan kamar yadda ya ke a kunshe a tsarinnan da ake kira da “SDGs – 4” a wani mataki na samar da ilimi mai inganci kuma ya kunshi kamai da komai wato Boko da Arabiyya.

A hirar sa da Yan Jaridu jimkadan da yin ziyarar, Shugaban Hukumar Almajiri na Kasa, Idris Muhammad Sani cewa ya yi makasudin wannan ziyara shine domin ya nemi hadin kai na Majalisar Wakilai musamman Kwamimitin na Ilimi na Musamman wanda shike da alhakin bibiyar Hukumar ta sa wajen ganin sun cimma burin da ya sa aka kafa Hukumar.

Muhammad Sani ya nuna matukar farin cikin sa ganin yadda Shugaban Kwamitin ya karbe su da kuma irin kishin da ya nuna na ganin ya bayar da gudunmawar da ake bukata wajen  ganin an mayar da miliyoyin yaran da ba sa zuwa makaranta, makaranta.

Ya ce irin kishin da ya gani da tsare-tsare da Majalisar take da shi ya kara masa kwarin gwiwa cewa lallai akwai kyakkyawan fata ga Almajirai da wadanda basa zuwa makaranta cewa su ma za a dama da su wajen gina Najeriya wacce kowa zai yi alfahari da ita.

Shugaban Hukumar ta Almajiri ya kara da cewa burin sa shine ya ga ya nemi hadin kan Yan Najeriya wajen ganin sun fahimci manufar Hukumar domin su bata goyon bayan da su ke bukata wajen ganin an gina al’umma wacce ita ma za ta bayar da gudunmawa wajen gina Kasarnan.

Sani, ya kara da cewa abun da ya ke gabansa shi ne ya zagawa kasarnan tahanyar ziyartar Jihohi 36 harda Abuja domin ganawa da Gwamnoni da Sarakuna da Kungiyoyin Al’umma da ma su fada aji wajen ganin sun marawa wannan yunkuri na Gwamnatin Taraiya na mayar da yara zuwa makaranta.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here