Home Tsaro Majalisar Wakilai Ta Umarci Hukumomin Tsaro Da Su Magance Satar Mutane, Kayan...

Majalisar Wakilai Ta Umarci Hukumomin Tsaro Da Su Magance Satar Mutane, Kayan Wutar Lantarki A Makarfi

132
0
20230720 102620
Majalisar Wakilai ta Umarci Hukumomin tsaro na Farin kaya, Jami’an Yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su kara sa ido akan kayayyakin wutar don hana bata gari satar kayan da lalata su.
Wannan mataki ya biyo bayan wani kuduri ne da Dan majalisa Mai wakiltar Makarfi da Kudan a majalisar Alhaji Umar Shehu Ajilo ya gabatar akan matsalar wutan lantarki da ta addabi  mazabrsa na lokaci mai tsawo.
Hon. Ajilo ya bukaci jami’an tsaro da su rinka yin sintiri na musammam akan manyan layukan wutan lantarkin kasarnan don hana bata gari lalatawa da sace wayoyin wutar lantarki.
Ya ce irin wadannan sace – sace sun haifarwa mazabarsa barazana ta tsaro da matsi na tattalin arziki.
Ajilo ya kara da cewa an kashe mutane da dama a yankin nasa ta hanyar buge su da daddare a kwace musu ababen hawa.
Dan Majalisar ya bukaci jami’an tsaro da su tallafawa yunkurin jami’an tsaro da ke yankin don maganta barazanar tsaro da ta addabi su.
Bayan haka sakamakon rashin wutar lantarki barazanar tsaro ta kara tsamari a yankin na sa yadda yan fashin daji suka koma yankin don gudanar da sana’ar su a yankin.
Sa bo da haka ya bukaci hukumomin samar da wutar lantarki na kasa da su gaggauta bincika dalilin rashin wutar lantarki a yankin don mayor da ita.
Majalisar Wakilan ta Umarci jami’an tsaro da Hukumar samar da wutar lantarki na kasa da su gaggauta daukar matiki na samar tsaro da wutar lantarki a yankin.
Har ila, yau ta umarci Kwamitin Wutar Lantarki da na Tsaro da za a kafa da su bibiyi lamarin don tabbatar da an kawo karshen  matsalolin da su ka addabi yankin baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here