Home Cinikaiyar Zamani Majalisar Wakilai Ta Umarci Babban Bankin Najeriya Da Ya Fito Da...

Majalisar Wakilai Ta Umarci Babban Bankin Najeriya Da Ya Fito Da Tsarin Fara Amfani Da Kudin China, Yaun

164
0
Hon. Leko

Majalisar Wakilan Najeriya ta umarci Kwamitocin ta ma su kula da Bankuna da harkokin kudade da su tattauna da Babban Bankin Najeriya don su lalubo  hanyoyin da su ka da ce, da manufofi, da za su taimaka wajen ganin Kasarnan ta fara amfani da Kudin China wato Yuan don gudanar da kasuwanci.

Majalisar ta bayar da wannan umarni ne sakamakon wani Kuduri na bukata da Hon. Jafaru Gambo Leko da ga Jihar Bauchi ya gabar a zauren Majalisar a ranar Larabar.

A yayin da ya ke yiwa Yan Jaridu Karin haske akan dalilin sa na gabatabat da wannan Kuduri ya ce ya lura da yadda Dalar Amurka ta zamarwa Yan Najeriya barazana ga kasuwancin su kai, harma da rayuwar su baki daya shi ya sa ya gabatar da wanna Kuduri.

Ya kara da cewa, Dalar Amurka ta shafi komai na ruyuwar Yan Najeriya in da duk abun da ake sayarwa sai a ce farashin sa ya tashi sabo da tashin farashin Dalar. “Hatta kayayyaki da ake nomawa a Najeriya sai a ce farashin su ya tashi sa bo da tashin farashin Dalar Amurka. Sabo da haka akwai bukatar mu sama mata kishiya don farashin ta ya karye”.

Ya ce Yan Najeriya su na gudanar da Kasuwanci iri daban-daban da Kasar China. Sa bo da haka idan aka sami yarjejeniya da Kasar China da Najeriya wajen amfani da Yuan. To lallai farashin Dala zai karye tun da bukatar ta zai ragu.

Hon. Jafaru ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya na samun koma baya sakamakon faduwar  darajar Naira, wanda ya haifar da tabarbarewar tattalin arziki da rashin tabbas.

Har ila yau, ya lura cewa asusun ba da lamuni na duniya IMF ya ba da shawarar fadada hanyoyin amfani da kudaden ketare ga manyan bankunan kasashe masu tasowa, ciki har da Najeriya.

Bugu da kari, ya ce  yanayin tattalin arzikin duniya yana kara habaka, kuma yanayin cinikayyar kasa da kasa na canjawa, in da kasar China ke kan gaba wajen ba da gudunmawa a  harkokin cinikayya a duniya;

Ya ce sanin kowa ne  kasar China tana da takardun Kudi da farashin su ya daidaita a kasuwannin duniya da kuma karbuwa a duniya, wato Yuan, wanda ke samun karbuwa a harkokin cinikayyar kasa da kasa a duniya.

Hon. Leko ya ce a busa wadannan dalilai ne Majalisar Wakilai ta umarci Kwamitocin ta na Kudi da na Bankuna da su tattauna da Babban Bankin Najeriya don samar da wannan yanayi da zai bayar da damar yin amfani da Kudin China wajen gudanar da kasuwanci a kasarnan.

Dan Majalisar ya kara da cewa Majalisar ta taba amincewa da irin wannan bukata a shekara ta 2018 amma ba’a bibiyi Kudurin ba. Amma a wannan karon Majalisar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin wannan Doka ta tabbata don samawa Yan Najeriya sauki.

Ya ce yin amfani da Kudin Yuan na kasar China zai zama wani mataki ne na rage faduwar darajar Naira tare da sama mata karayi a kasuwar Duniya. In da ya kara da cewa kasashen da su ke kewaye da Najeriya kamar su Nijar da Kamaru da Chadi kudaden su sun fi namu daraja sabo da su na amfani da kudin Faransa wato Saifa.

Har ila yau, ya ce kawancen da ake bukata don yin amfani da kudin Yuan na kasar China a matsayin kudaden da Gwamnatin Taraiya za ta rinka amfani da su don musayar kudaden  ajiyar kasashen waje a hukumance zai taimaka mutuka wajen gudanar da kasuwanci tsakanin Najeriya da Kasar China.

Daga karshe Majalisar ta bukaci kwamitocin kula da Bankuna da harkokin kudade da su gana da Babban bakin Najeriya CBN domin duba yiyuwar aiwatar da hakan ka na Kwamitin ya gabatar da rahoton sa cikin makonni hudu domin daukar mataki na gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here