Home Uncategorized Majalisar Wakilai Ta Umarci A Bincika Dalilin Watsi Da Aikin Samar Da...

Majalisar Wakilai Ta Umarci A Bincika Dalilin Watsi Da Aikin Samar Da Wutar Lantarki Ta Hanyar Iska A Jihar Katsina

89
0
Hon. Banye

Majalisar Wakilai ta umarci Kwamitin ta na Wutar Lantarki da ya tuntubi Ma’aikatar Wutar Lantarki ta Kasa domin ya binciki daliliin da ya saka a ka yi watsi da aikin wutar lantar da aka fara yi tun lokacin Marigayi Tshohon Shugaban Kasa, Umaru Musa Yar’adua a Lambar Rimi da ke Jihar Katsina don kammala aikin.

Majalisar ta bayar da wannan umarni ne a sakamakon wani Kuduri na gaggawa da Dan Majalisar Wakilai mai Wakiltar Kananan Hukumomin Batagarawa da Chiranci da Rimi, Hon. Murtala Usman Banye ya gabatar a zauren Majalisar a ranar Laraba.

A yayin da Dan Majalisar ya ke yiwa Yan Jaridu karin haske a kan Kudurin, Hon. Banye ya ce wannan aiki na samar da Wutar Lantarki ta hanyar amfani da Iska na da ga cikin Yunkurin Tsohon Shugaban Kasar, Marigayi Yar’dua na samar da Wutar Lantarki don magance matsalar da ta ki taki cinyewa shekara da shekaru a Najeriya.

Ya ce wannan aiki na da ga cikin aiyuka mafi girma da a ka taba samarwa a kasashen Africa na samar da Wutar Lantarki ta hanyar Iska da zai samar da megawatt 10, wanda aikin sa ya kai kimanin kashi 90 na kammalawa amma aka yi watsi da shi bayan rasuwar Shugaban Kasa, Umaru Musa Yar’adu.

Hon. Banye ya nuna irin mahimmanci da aikin ya ke da shi na samawa kananan masana’antu wutar Lantarki wanda hakan zai samar da cigaba na bunkasa tattalin arzikin Yan Najeriya da samar da aikin yi ga dubbin matasa da ke kasarnan, watakila harma da kasashe makota.

Ya nu na takaicin sa na watsi da wannan aiki wanda ya ce har kayayakin da a ka kafa sun fara lalacewa sakamakon halin ko in kula da a ka nu na da aikin. Sabo da haka ne ya gabatar da wannan kuduri domin a tabbatar da an kammala wannan aiki domin tallafawa Yunkurin Gwamnati na samar da wutar Lantarki a Kasarnan.

Dan Majalisar ya kara da cewa wannan mataki da ya dauka zai ba shi dama na ya tunkari Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda domin su hada karfi da karfe don tunkarar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu don su ga an kammala wannan aiki domin amfanar Yan Najeriya musamman a wannan lokaci da matsalar wutar Lantarki ta ki ci taki cinyewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here