Home Ilimi Majalisar Wakilai Ta Shawarci Gwamnatin Taraiya Da Ta Dakatar Da Karin Kudin...

Majalisar Wakilai Ta Shawarci Gwamnatin Taraiya Da Ta Dakatar Da Karin Kudin Makarantar Kwalejen Taraiya

163
0
Hon. Misau, Bauchi

Majalisar Wakilai ta Shawarci Gwamntain Taraiya da ta dakatar da Karin kudin Makarantar Kwalejin  Taraiya ta wato “Unity School” musamman a wannan lokaci da ake fama da matsi na tattalin arziki.

Majalisar ta bayar da wannan shawara ne ranar Alhamis  bayan da Dan Majalisar Wakilai da ga Jihar Bauchi, Hon. Aliyu Baffa Misau ya gabatar da bukata ta musamman a gaban majalisar.

Ya yin da ya ke gabatar da Kudurin Hon. Misau ya ce baikamata ba a kara kudin makarantar sabo da matsi da ake ciki na tattalin arziki sakamakon Karin kudin man fetur da akayi wanda hakan ya kara ta’azzara kuncin rayuwa ga Yan Najeriya.

Hon. Misau ya ce talaka da ma da kar yake iya yin karatu, barantana da aka cire tallafin Man Fetur wanda ya haifar da tashin gwauron zabi na farashin kayayyaki na rayuwa;

A hirarsa da Jaridar Viewfinder, Hon. Misau ya ja hankalin wadanda suke mulkin kasarnan akan cewa kusan dukkannin su a kauta sukayi karatu a kasarnan sa bo da haka baiga dalilin da za su tsauwalawa harkar neman Ilimi ba a kasarnan.

“ Ni kai na gwamnati ta dauki nauyi karatu na tun da ga firamare harzuwa Jami’a sabo da haka banga dalilin da zai sa, dan tallafin da ake bayarwa a Unity Schools ba za a tsauwala shi”.

Ya ce a Unity School ne ake bawa dan talaka dama domin ya cimma burin sa ba tare da lakari da in da mutum ya fito ba. In da ya ce idan aka tsauwala kudin makarantar to za a kori ‘yayan talakawa da ga makarantar.

Hon. Misau, ya ce ya kuduri niyya kare hakkin talaka “ in Kunga dama za ku iya kira na Jagoran Talakawa na Najeria, zanci ga ba da fafutuka na ganin wannan Karin bai tabbata ba a matsayina na shugaban Kwamitin Ilimi wato TETFUND”

A wani bangaren kuma, Hon. Misau ya ja hankalin Hukumar NNPC da hukumomi da ke kula da harkar Mai da su fito da wata hanya ganin an daina kona Iskar Gas a banza kasarnan. In da ya ce ya gabatar da Kuduri akan wannan batum ma ganin yadda ake asarar biliyoyin kudi ta hanyar Kona Iskar Gas a kullum a Najeriya.

Ya ce idan an sarrafa Iskar Gas za a iya amfani da ita wajen bukatum yau da kullum sabo da haka ya zama wajibi a daina kona Iskar shekara da shekaru; in da ya ce lokaci ya yi da za a sarrafa Iskar don saukakawa Yan Najeriya wajen girke girke da samar da wutar lantarki.

Hon. Misau ya shawarci Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya fadada tunanin sa  na ganin an sarrafa Iskar Gas din domin saukakawa Yan Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here