Home Uncategorized Majalisar Wakilai Ta Sha Alwashin Karya Farashin Siminti A Kasarnan

Majalisar Wakilai Ta Sha Alwashin Karya Farashin Siminti A Kasarnan

136
0
Hon. Gaza

Majalisar Wakilai ta ce zata yi duk mai yiwuya don ganin farashin Siminti ya sauka a kasarnan ganin cewa dukkannin abubuwan da ake amfani da su wajen yin sa da ga kasarnan ake samun su.

Dan Majalisar Wakilai Hon. Jonathan Gaza da ga Jihar Nasarawa ne ya sanar da haka jimkadan da dage zaman Kwamitin Ma’adanai domin ya bawa Ministan Ma’adanai da sauran ma su ruwa da tsaki dama su halarci zaman Kwamitin don jin dalilin da ya sa farashin Siminti ya ke tashi a kasarnan.

Hon. Gaza ya ce babu wani dalili da zai sa farashin ciminti ya rinka tashi ba kai ba gindi a kasar da take da ma’adanai da ake bukata don yin siminti. Ya ce Allah ya albarkaci kasarnan da ma’adanai masu yawa da ya kamata ace Yan Najeriya su na cin amfanin arzikin da Allah ya yiwa kasarnan amma sai wasu su zo daga wata kasar su kwashe su yi tafiyar su.

Dan Majalisar ya kara da cewa Majalisar Wakilai za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta hada kan duk masu ruwa da tsaki akan harkar Siminti domin taji dalilin da ya sa farashin ya ke ta shi don magance matsalar.

Hon. Gaza ya nuna mahimmanci siminti wajen gina gidaje na zamani da na gargajiya in da ya kara da cewa ko a ginin gargajiya ana amfani da Siminti wajen ginin kasa a wani mataki na karfafa shi don ya yi karfo.

Kwamitin ya umarci Ministan Ma’adanai da sauran masu ruwa da tsaki akan harkar Siminti da su tabbatar sun baiyana a gaban Kwamitin nan da sati biyu masu zuwa kuma Kwamitin ba zai karbi wani uzuri  da ga gare su ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here