Home Siyasa Majalisar Wakilai Ta Sha Alwashin Ganin An Samu Sauki A Farashin Aikin...

Majalisar Wakilai Ta Sha Alwashin Ganin An Samu Sauki A Farashin Aikin Hajji Na Shekara Mai Zuwa

129
0
Hon. Ajilo

Majalisar Wakilai ta ce za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin an samu sauki akan Kudin da ake so a saka na Aikin Haji da ake so a saka shekara mai zuwa a wani mataki na saukakawa Yan Najeriya musamman ganin yadda ake fama da matsi na tattalin arzikin kasa.

Dan Majalisar Wakilai mai Wakiltar Makarfi da Kudan da ke Jihar Kaduna, Honorabul, Umar Ajilo ne ya sanar da haka ga Yanjaridu bayan da Kwamitin Aikin Hajji ya gana da masu ruwa da tsaki akan harkar a satin da ya gabata.

Ya ce Majalisar ta yi duba da halin da ake ciki na matsi na tattalin arziki kuma ta ga ya dace a saukakawa Yan Najeriya wajen sauke farali ga wanda Allah ya horewa. Sabo da haka ya ce majalisar ta dukufa wajen ganin an samu sauki a farashin da za a saka na hajjin badi.

A wani bangaren kuma, Dan Majalisar ya gabatar da wani kuduri wanda Majalisar ta amince da a umarci Kamfanin DSTV, masu haska fina-finai da su  dakatar da Karin farashin da su ka yi a wani mataki na saukakawa Yan Najeriya duba da halin da ake ciki na matsin tattalin arzikin kasa.

Ajilo ya ce a fannin kallo kawai Yan Najeriya suke samun sauki idan aka lura da irin matsi na tattalin arziki da ake ciki ta hanyar kallon wasannin kwallo da fina-finai.

Ya ce idan wannan bangare ma aka matsa, ta ina Dan Najeriya zai samu sauki.

Sabo da haka ne Majalisar ta amince da wannan bukata domin a samawa Yan Najeriya sauki a fannin nishadin rayuwa.

Har ila yau, a bangaren sufuri ma Hon. Ajilo ya gabatar da bukatar da bukata ga Ministan Sufuri dangane da a rage farashin tikitin Jirgin kasa da ake caza a halin yanzu da ga Abuja zuwa Kaduna a wani mataki na saukakawa Yan Najeriya.

Ya ce sakamakon cire tallafin Mai da aka yi akwai bukatar ganin an saukakawa Yan Najeriya ta hanyar rage farashin tikitin. Bayan haka, ya nemi Ministan da ya duba ganin yiwuwar ganin an kyale wanda ya rasa Jirgin da ya bukata ta hanyar yin amfani da tikitin na sa a wani jirgin na gaba.

Dadin dadawa, Dan Majalisar ya bukaci Ministan da ya yi gyare gyare a jiragen da ake amfani da su. Inda ya ce ya lura cewa wasu gilasai na jiragen sun fashe sabo da haka akwai bukatar ayi gyara a taragun jiragen don kare lafiyar fasinjojin da samar da yanayi na nutsuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here