Home Tsaro Majalisar Wakilai Ta Bukaci Gwamnatin Taraiya Da Ta Samar Da Rundunar Sojoji...

Majalisar Wakilai Ta Bukaci Gwamnatin Taraiya Da Ta Samar Da Rundunar Sojoji A Yankin Gusau/Tsafe

131
0
Hon. Mai Palace

Majalisar Wakilai ta bukaci Gwamnatin Taraiya da ta girke rundunar Sojiji a yankin Gusau da Tsafe da ke Jihar Zamfara a wani mataki na kawo karshen hare-haren Yanta’adda da ya yi tsamari a yankin.

Majalisar ta gabatar da wannan bukata ne satin da ya gabata sakamakon wani Kuduri na gaggawa da Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar kananan Hukumomin Gusau da Tsafe, Hon. Kabiru Ahmad Mai Palace da ya gabatar a zauren Majalisar.

A ya yin da yake yiwa Yan Jaridu Karin haske akan Kudurin jiya Talata, Mai Palace ya ce wannan bukata ta na da mutukar mahimmanci gaske ga al’umar yankin na sa domin hare-haren Yanta’addan ya kai mutuka wanda satin da ya gabata sun kashe mu su mutum 27 a garin Bilbis tare da jikkata gomman mutane da kuma yin awun gaba da wasu kimanin mutum 40.

Ya ce rayuwa ta yi tsanani a yankin in da Yan ta’addda su na iya shiga kowanne gari ko da  wanne lokaci su yi abun das u ke so, su yi tafiyar su ba tare da shakkar kowa ba.

Mai Palace ya kara  da cewa duk da yake akwai shinge na jami’an tsaro kusan guda goma da ga Funtua da ke Jihar Katsina zuwa Gusau da ke Jihar Zamfara, hakan baya hana Yanta’addan su aikata barnar su tsakanin shingayen na kimanin awowi biyu su yi kuma tafiyar su ba tare da wani jami’in tsaro ya ce musu uffan ba.

Bayan haka, Hon. Mai Palace cewa ya yi a halin yanzu mutanen Yankin na sa su na barin garuruwan su  domin su tsira da rayukan su da dukiyoyin su. Ya kara da cewa an hana mutanen yankin sakat ta yadda manomi bai isa ya je gona ba; idan ma ya je ya noma abun da ya noma ya zama mallakar Yanta’addan.

Dan Majalisar ya cigaba da cewa a halin da ake ciki yanzu duk wani mai kimanin naira miliyan daya zuwa biyu ya bar kauyukan da  su ke yankin Gusau/Tsafe ya koma birni domin Yanta’addan sun tatike duk wani mai hali da ya ke kauye wanda hakan ne yasa su ke kawo hari cikin birane.

Hon. Kabiru Mai Palace ya ce wannan dalili ne ya sa ya gabatar da Kuduri na gaggawa a gaban Majalisar Wakilai a matsayin sa na wakilin Jama’ar sa domin Gwamnatin Taraiya ta kawo mu su dauki tunda ita take da iko da Sojoji da Yansanda da sauran jami’an tsaro da ke kasarnan.

Ya ce ya na da kyakkyawan yakini cewa wadannan Yanta’addan ba su fi karfin Gwamnati ba. Idan an yi niyyar yakar Yanta’addan za’a iya cikin kankanin lokaci.

A daya bangaran kuma ya ce Gwamnatin Jiha tana yin iyakacin kokarinta na samar da Jami’an Tsaro na Sakai, amma ya ce hakan ba zai wadatar ba duk da cewa su na yin iyakacin kokarin su na tallafawa Jama’an Tsaro da bayanai da suaran su.

Hon. Kabiru Mai Palace ya yi kira ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin sa na Shugaban Askarawan Najeriya da ya dubi Allah ya taimakawa Jihar Zamfara dama jihohin da ake fama da matsalar Tsaro na yakar Yanta’addan nan da dukkan karfin sojan da ya kamata a wani mataki na samar zaman lafiya da kwanciyar hankali da arziki mai dorewa a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here