Home Zirga zirga Majalisar Wakilai Ta Bukaci Gwamnatin Taraiya Da Ta Gaggauta Gyara Hanyar Da...

Majalisar Wakilai Ta Bukaci Gwamnatin Taraiya Da Ta Gaggauta Gyara Hanyar Da Ta Tashi Da Ga Kano Zuwa Bauchi

160
0
Hon. Ranga

Majalisar Wakilai ta bukaci  Gwamnatin Taraiya da ta gaggauta gyaran hanyar da ta tashi da ga Kano  da Jigawa zuwa Bauchi sakamakon yawan mutane da suke rasa rayukan su a kullum  a bisa rashin kyaun hanyar.

Hakan ya biyo bayan wani kuduri na bukata da Dan Majalisar Wakilai mai Wakiltar Ningi da ga Jihar Bauchi, Hon. Adamu Hashimu Ranga ya gabatar a satin da ya gabatar a zauren Majalisar.

Hon. Ranga ya ce titin tun da aka gina shi a 1980’s ba a sake waiwayar titun ba sai a lokacin PTF.  Sabo da haka titun ya yi mutukar mutuwa wanda hakan ya sa a kullum sai an yi hadari da yake saka a rasa rayuka da dukiya ma su yawa.

Majalisar ta bukaci Ma’aikatar Aiyuka da Hukumar FERMA da su gaggauta kaiwa titin dauki domin a dakatar da asarar da ake yi a kullum.

Hon. Ranga ya kara da cewa bayan rayuka da ake rasawa titun ya na da mutukar muhimmanci domin kuwa ya hada manya garuruwa da suka hada da Kano da Jigawa da Bauchi da Adamawa da Gombe da Jos sabo da haka akwai bukatar a gaggauta gyara shi sabo da kasuwanci da ake gudanarwa a kan titin.

Dan Majalisar ya yiwa Yan Jaridu Karin haske cewa Majalisar bayan tayi kuduri zata saka ido ta hanyar bibiya wajen ganin an gaggauta gyaran hanyar sabo da muhimmanci da titin ya ke da shi ga garuruwan da su ke amfani da hanyar.

Hon. Ranga ya roki mutanen da ke Mazabar sa da duk wadan da suke amfani da hanyar da su kara hakuri a ya yin da Majalisar Wakilai za ta cigaba da bibiya wajen ganin an gaggauta gyaran hanyar cikin kankanin lokaci.

A wani bangaren kumka, Hon. Ranga ya ce ya yi shiri na musamman wajen ganin ya inganta ruywar matasa da mata a yankin sa in da zai bayar da tallafin Ilimi ga matasa 50 in da su kuma mata zai tallafawa mu su da inji na 268 domin su gudanar da sana’o’i daban daban wanda aka kiyasta za ‘a kashe kudi kimanin Naira miliyan 100.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here