Home Kwadago Majalisar Wakilai Ta Bukaci Da A Ware Kaso 30 Na Gurbin Aiki...

Majalisar Wakilai Ta Bukaci Da A Ware Kaso 30 Na Gurbin Aiki Ga Ma Su Aikin Sa Kai Na Yansanda Da Sibil Difens

127
0
Hon. Gumi 2

Majalisar Wakilai ta bukaci Ma’aikatar Cikin Gida da ke kula Hukumar Yansanda da Sibil Difens da ta yi naziri a kan yiwuwar samar da wani kaso na gurbi don daukar matasa da su ke yin aikin sa kai na Yansanda da Sibil Difens domin a ba su guraben aiki na dindindin.

Majalisar ta bayar da wannan shawara ne a sakamakon wani kuduri da Dan Majalisar Wakilai, mai Wakiltar  Kananan Hukumomin Gumi da Bukuyum da ga Jihar Zamfara, Hon. Sulaiman Abubakar Mahmud Gumi ya gabatar a zauren Majalisar a ranar Laraba.

Kudurin wanda ya bukaci Ma’aikatar Cikin Gida da ke kula da hukumar Yansanda da ta duba yiwuwar ware a kalla kaso 30 na guraben aiki ga mutanen da su ka sadaukar da rayuwar su wajen tallafawa Yansanda ta hanyar aikin sa kai a wani mataki na karfafa mu su gwiwa na bautawa kasar su wajen magance matsalar tsaro da ta addabi kasarnan.

Hon. Gumi wanda ya ce dalilin sa na gabatar da wannan Kuduri shi ne ya lura da irin gudunmawar da masu aikin sa kai su ke bayarwa amma da ga bisani idan an zo daukar aiki Yansanda sai a yi watsi da su, a maimakon a saka su da ga cikin wadanda za su amfana da wannan dama ta bautawa kasar su da al’ummar su.

Ya ce idan aka amince da wannan tsari zai taimaka wajen sakawa Yan kasa kishi na bautawa kasar su ta hanyar yin aikin sa kai kafin su sami aikin yi bayan sun kammala karatun su. Bayan haka, zai kuma tallafa wajen samar da Yansanda ingantattu wadan da su ka samu horo da ga Yansanda ko  Sibil Difens ta hanyar zaben wadanvda su ka samu takardar yabo da ga gare su.

Hon. Gumi ya kara da cewa idan a ka fito da wannan tsari zai ja hankalin matasa na da su bautawa kasarsu da al’umar su kafin su sami aikin yi ko kuma ya zama wata hanya ta samun aikin yi cikin sauki a maimakon mutum ya yi ta jirar aiki shekara da shekaru.

Dan Majalisar ya cigaba da cewa wannan tsari har ila yau zai taimakawa su kan su Yansandan na zabar wadanda su ka dace tare da samun horo tun gabanin a dauke su aikin Dansanda.

Dag a karshe Majalisar ta amince da dukkan bukatun da Dan Majalisar ya gabatar na yin duba na tsanaki akan wannan bukata tare da bukatar Kwamitin Ma’aikata Cikin Gida da ke da alhaki da Harkumar  Yansanda da ya bibiyi wannan batu domin ganin an amince da shi ya zama doka don amfanar Yan Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here