Home Kotu da 'Yan sanda Majalisar Taraiya Ta Yabawa Tinubu Da Ya Karawa Yansanda Kudi Da...

Majalisar Taraiya Ta Yabawa Tinubu Da Ya Karawa Yansanda Kudi Da Ga Naira Biliyan 5 Zuwa 16

218
0
20231214 142114

Malisar Taraiya ta yabawa Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu da ya karawa Hukumar Yansanda kudi da ga Naira Biliyan 5 a shekara ta 2023 zuwa naira Biliyan 16 a shekara ta 2024 a kasafin kudin da ya gabatar ga Majalisar.

Shugaban Kwamitin Yansanda na Majalisar Wakilai, Hon. Makki Abubakar Yanleman ne ya yi wannan yabo bayan kammala sauraron kasafin kudi
 na Hukumar da Kwamitin na hadaka ya gudanar yau Alhamis a zauren Majalisar.
 Ya ce Majalisar na ganin wannan yunkurin zai taimaka wajen ganin an sami ingantaccen tsaro a Kasarnan.
Hon. Makki ya kara da cewa Majalisar za ya saka ido wajen ganin kudade da aka warewa Hukumar a kasafin kudin na shekara ta 2024 an kashe su kamar yadda aka tsara domin ganin an inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
Dan Majalisar ya ce Majalisar ta  gamsu da yadda Hukumar Yansanda ta kashe kudaden da aka bata a shekara ta 2023. Sabo da haka za ta duba yiwuwar ganin an karawa Yansanda kudade domin tsaro shine kashin bayan kwanciyar hankali da yalwayar arziki.
Har ila yau, Hon. Makki ya ce za su kuma saka ido wajen ganin an sayi makamai na zamani tare da inganta rayuwar Yansanda ta hanyar ba su hakkokin su. ” su ma mutane ne. Ya yin da muna gidajen mu muna barci, su kuma sun hana idon su barci domin mu zauna lafia”.

Makki ya yi kira ga Yan Najeriya da su bawa Yansanda goyon baya da hadin kai ta yadda za a sami kwanciyar hankali da zaman lafiya a Kasarnan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here