Home Ilimi Majalisar Taraiya Ta Bukaci Da A Samar Da Sabuwar Manhajar Koyo Da...

Majalisar Taraiya Ta Bukaci Da A Samar Da Sabuwar Manhajar Koyo Da Koyarwa A Jami’o’in Kasarnan

240
0
Mai Palace

Majalisar Wakilai ta umarci Kwamitinta na ilimi mai zurfi da Hukumar da take Kula da Jami’o’I wato NUC da su hada kai domin yin gyara akan Manhajar koyarwa da ake amfani da ita a wani mati na zamanantar da koyo da koyarwa a kasarnan.

Majalisar ta bayar da wannan umarni ne a satin da ya gabata a sakamakon wani kuduri na gaggawa da Dan Majalisar Taraiya mai Wakiltar Gusau da Tsafe da ga Jihar Zamfara, Hon. Kabiru Ahmadu Mai Palace ya gabatar.

Hon. Mai Palace ya ce dalilin sa na kawo wannan kuduri shi ne ya lura da yadda  duniya ta canza amma Najeriya ta na amfani da manhaja da aka kirkirota sama da shekaru 30 da suka wuce kuma ta kasa samar da mafita na kalubale da kasarnan ta ke  fuskanta.

Sabo da haka ne ya bukaci Majalisar da ta umarci Kwamitin Ilimi mai zurfi na Jami’a da Hukumar Kula da Jami’o’I da su zauna su hada kai domin su lalubowa da kasarnan Manhaja da ta yi daidai da zamani da kuma irin bukatar da kasarnan ta ke da ita.

Dan Majalisar ya ce zamani ya zo da canje-canje na yadda ake koyarwa ta hanyar yin amfani da na’urori na zamani da kuma yanar gizo-gizo. Sabo da haka Najeriya ya kamata ta canza yadda ake koyar da al’umar ta ta yadda za su  amfani kasa da kayukan su baki daya.

Ya ce Manhajar, akwai bukatar ta bayar da ilimi wanda zai koyar da sana’o’I da matasa za su dogara da kan su wajen samawa kansu aiki ba tare da  dogara da gwamnati ba don samawa kan su aikin yi.

Mai Palace ya ce Najeriya ta na kwararru da ma su ilimi da za su kawo gyaran da a ke bukata domin ya je wata Kasa a nahiyar Turai in da ya samu wani dan Najeriya ya na jagorantar Kasar domin samawa kasar sabuwar Manhaja ta koyo da koyarwa wanda hakan ne ya bashi kwarin gwiwa wajen gabatar da wannan kudurin ganin cewa in yan Najeriya za su samawa wata kasa mafita mai zai hana su samawa kan su.

Majalisar Wakilan ta bawa Kwamitin na ta sati biyu da ya tuntubi Hukumar kula da Jami’o’I ta kasa (NUC) da su zauna don fara shirin samawa kasarnan sabuwar Manhaja da zata kawo cigaban da ake bukata a kasarnan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here