Home Tsaro Majalisar Najeriya ta ƙi amincewa da buƙatar Tinubu ta tura sojoji Nijar

Majalisar Najeriya ta ƙi amincewa da buƙatar Tinubu ta tura sojoji Nijar

161
0
Senate Plenary 3

‘Yan Majalisar Dattawan Najeriya sun ƙi amincewa da buƙatar neman goyon bayansu da Shugaba Bola Tinubu ya aika kan tura sojojin ƙasar zuwa Nijar don tilasta wa sojoji komawa kan tsarin mulki.

Shugaba Tinubu ya nemi goyon bayan ‘yan majalisar ne cikin wata wasiƙa da ya aika musu ranar Juma’a, inda ya bayyana musu matakan da ya ɗauka a matsayinsa na shugaban ƙungiyar Ecowas ta raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma.

Bayan fitowa daga wani zaman sirri a ranar Asabar, Majalisar ta jaddada goyon bayanta ga yunƙurin Ecowas, ban da maganar amfani da ƙarfin soja.

“Mun ƙi amincewa saboda ba abu ne da ya kamata a fara tunaninsa ba ma, saboda abu ne na cikin gida,” kamar yadda Sanata Ali Nudme ya shaida wa BBC.

Sanatan ya ƙara da cewa shawarar da mafi yawan sanatocin suka bayar ita ce a ci gaba da yunƙurin sulhu ta hanyar difilomasiyya, maimakon ƙarfin soja.

“Muna da shugabannin ƙasa, waɗanda sojojin Nijar ke mutuntawa kamar Buhari da Abdulsalam da Babangida da Jonathan, idan aka yi amfani da waɗannan za a samu masalaha,” a cewarsa.

Cikin matakan da Tinubu ya ɗauka akwai kulle iyakokin Najeriya da Nijar, da katse wutar lantarkin da ƙasar ke samu daga Najeriya, da dakatar da hulɗar kasuwanci, kamar yadda Ecowas ta cimma a zaman da ta yi a Abuja.

Kwamashinan zaman lafiya da difilomasiyya na Ecowas, Dr Abdel-Fatau Musah, ya faɗa wa BBC Hausa cewa suna ci gaba da bin hanyoyin difilomasiyya wajen sasanta rikcin.

“Muna ci gaba da tura tawagar tattaunawa, idan ba su [sojojin juyin mulki] bari ba kuma to shugabannin mambobin ƙasashen ne za su faɗa mana abin da ya kamata mu yi,” a cewarsa bayan kammala taron manyan hafsoshin tsaro na Ecowas ranar Juma’a.

Ƙasar Faransa, wadda ta yi wa Nijar mulkin mallaka, ta bayyana goyon bayanta ga yunƙurin Ecowas, yayin da sojojin Nijar ɗin suka bayyana soke dukkan yarjejeniyoyin tsaro tsakaninsu da tsohuwar uwargijiyar tasu.

Sai dai kuma, ƙungiyoyi da wasu fitattun ‘yan Najeriya na ci gaba da gargaɗin Shugaba Tinubu game da amfani da ƙarfin soja kan Nijar, suna masu nuna fargaba kan matsalolin tsaron da ƙasashen biyu ke ciki.

Tuni sojojin juyin mulkin suka ba da sanarwar soke hulɗar jakadanci tsakanin Nijar da ƙasashen Faransa da Togo da Najeriya da kuma Amurka.

A ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa suka sanar da kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum bayan sun tsare shi a fadar.

Kamar a maƙwabtanta Burkina Faso da Mali, kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum da sojoji suka yi ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani ya zo ne daidai lokacin da ake ƙara tsanar Faransa a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here