Home Labaru masu ratsa Zuciya Majalisar Datttawa Ta Amince Da Hukuncin Kisa Kan Masu Ta’ammali Da Muggan...

Majalisar Datttawa Ta Amince Da Hukuncin Kisa Kan Masu Ta’ammali Da Muggan Kwayoyi

138
0

Majalisar Datttawa ta amince da a zartar da20231013 125848 hukuncin Kisa a kan duk mutumin da aka kama  ya na  ta’ammali da Muggan Kwayoyi a Najeriya a wani mataki na ganin an dakile harkar.

Majalisar ta amince da wannan hukuncin ne bayan an gabatar da rahoton Kwamitin da ya yi gyara akan Dokar Ta’ammali  Da Muggan Kwayoyi ta Hukumar Kalu da Hana Fatauci da Ta’ammali da Muggan Kwayoyi ta Kasa wato NDLEA.
Bayan da Shugaban Kwamitin Gyaran,  Sanata Babagana Munguno ya gabatar da rahoton nasa, Sanata Ali Ndume ya Mike ya gabatar da bukatar na ayi gyara akan hukumancin durin rai da rai, a mayar da da shi hukuncin Kisa.
Anan ta ke  ne Mataimakon Shugaban Majalisar Dattawa , Sanata Barau Jibrin wanda ke jagorantar zaman Majalisar a lokacin ya ce da Ali Ndume me yake ci na baka na zuba tun da dai an gabatar da rahoton. Me zai hana a cigaba da amincewa kudurin daya bayan daya, idan da
gyara sai a yi kawai.
Nan take Majalisar ta rinka yin gyara  akan rahoton in da da aka  yanke hukuncin Kisa gurin da aka rubuta hukuncin daurin rai-da-rai akan duk wanda aka samu yana Ta’ammali da Mugegan Kwayoyi  sai a ka yi kuri’a domin a mayar da shi hukuncin Kisa.
Ko da ya ke an sami  dan hatsaniya akan masu goyon bayan daurin rai-da-rai da ma su goyon bayan hukuncin Kisa amma da ga karshe an amince da Hukuncin na Kisa a matsayin Doka.
Sanata Munguno ya yi wa Yan jaridu karin haske akan wannan sashen da su ka amince da Hukuncin Kisa in da ya ce duk wanda aka kama  ya na taimakawa wajen Ta’ammali da miyagun Kwayoyi ko sha ko sayarwa hukuncin Kisa za a zartar ma sa.
Ya kara da cewa wannan hukunci ya shafi Muggan Kwayoyi ne kawai kamar su Koken da Heren da dangin su banda su Wiwi da sauran kananan kayan Maye.
Bayan Hukuncin Kisa duk wanda a ka kama ya na ta’ammali da Muggan Kwayoyi za a kwace dukkan dukiyar da ya mallaka. Sai dai ita kuma hukumar NDLEA za a mallaka mata wani kaso na dukiyar sauran sai a saka a asusun Gwamnatin Taraiya.
20231102 145959
 Sanata Ali Ndume wanda shi ne ya kawo shawara akan a mayar da hukuncin rai-da-rai zuwa hukuncin Kisa cewa ya yi ya lura da cewa masu yin harkar sun raina hukuncin ne.
Sa bo da haka ya ce yana ganin daukar hukuncin Kisa zai sa ma su harkar su shiga taitayin su. Domin duk kasashen da su ke yaki da Muggan Kwayoyi da gaske hukuncin Kisa su ke zartar wa kamar su Saudi Arabia da China da Kwalambiya da sauran su.
Ndume ya ce ya na da masaniya cewa manyan Kasa da yayan Manya su ne akasarin ma su ta’ammali da Muggan Kwayoyi sabo da haka ne yace a ware a Majalisar ma su goyon bayan hukuncin Kisa da na rai-da-rai domin Yan Najeriya su ga karar a wadanda su ke goyon bayan harkar sai su ka zame.
Ya ce amincewa da wannan Doka babbar nasara ce domin irin illar da ta ke tattere da harkar na lalata rayuwar Yan Najeriya.  ” Wannan Jahadi ne ya kamata kuma Yan Jaridu ku bayar gudunmawa wajen yakar wannan harkar”. Inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here