Home Siyasa Majalisar Dattawa Za Ta Mallakawa Sanatoci 109 Titunan Gwamnatin Taraiya

Majalisar Dattawa Za Ta Mallakawa Sanatoci 109 Titunan Gwamnatin Taraiya

513
0
Sen. Hussaini 2

By: Madina Dauda,  Abuja

Shugaban Kwamitin Gyaran Titunan Gwamnatin Taraiya na Majalisar Dattawa Sanata Babangida Hussaini ya ce shirye shirye sun yi nisa na mallakawa Sanatoci 109 Titunan Kasarnan a wani mataki na ganin an kula da su kamar yadda ya da ce.

Dan Majalisar ya sanar da haka ne a hirar sa da Yanjaridu a ofishin sa da ke Abuja a ranar Laraba in da ya ce tuni ya sami amincewar sanatocin su 109 na a mallaka mu su titunan don su rinka kulawa da su san nan su rinka sanar da gwamnati halin da titunan su ke ciki akai-akai.

Sanata Hussaini, ya ce Gwamntain Taraiya ta na da tituna mallakar ta kimanin Kilomita 38,000  wadanda a ka yiwa kiyasi na daraja kimanin N18 Tiriliyan wadan da aka gina su kimanin sama da shekaru 50 da suka wuce. Sabo da haka, ya ce kashi 70 na titunan duk sun mutu.

Sanatan ya kara da cewa a bisa wannan dalili ne ya sa ya fito da wannan tsari na mallakawa Sanatocin wadannan titutun domin su saka ido wajen ganin an kula da titunan a lokacin da ya dace.

“ Titi na kowa ne, ba bu zancen addini ko siyasa ko kabila ko bangaranci. Kowa ya na amfani da titi. Sabo da haka, ya sa muka fito da wannan tsari domin mu nunawa Yan Najeriya cewa kowa ya na da hakki akan titi. Sabo da haka kula da shi ya dogara akan kowa da kowa ba tare da nuna wani bambanci ba”. In ji Hussaini.

Babangida Hussaini ya cigaba da cewa a sati mai zuwa zai gabatar da Kuduri a gaban Majalisar Dattawa akan wannan batu domin Kudurin ya sami amincewar Majalisar.

“Tuni Yan Majalisar su ka amince da wannan shawara da mu ka gabatar mu su, sun nuna gamsuwar sun a ganin wannan karramawa ce a ka yi mu su. Sabo da haka zan gabatar da Kuduri sati mai zuwa akan hakan”. In ji Shi.

Abu na gaba da Sanata Hussaini ya kuduri niyya shine mayarwa da FERMA aikinta na gyaran hanya kai tsaye kamar yadda yak e a baya. Ya ce da ga yanzu, Hukumar za ta daina bayar da kwangilar gyaran titi a maimakon haka, za ta rinka yin gyaran ne da kanta kai tsaye kamar yadda yak e a Dokar da ta kafata mai lamba (FERMA ACT. 72).

Ya ce Hukumar za ta daina jira sai an yi kasafin kudi kafin ta yi gyaran titi domin kuwa shi al’amarin titi ya na da lokaci, idan ba’ayi gyara a kan lokacin da ya dace ba toh za’ayi asarar lokacin. In da ya ce a kudu watanni uku kawai a ke da su domin aikin titi, a yayin da a Arewa a na da watanni 7 sabo da ruwan sama da a ke yi. Y ace, ya zama wajibi a gaggauta a kan gyaran titi domin a ci ribar lokacin da a ke da shi.

Ga me da gaiyata da a ka yiwa shugabannin Jami’an tsaro in da  Sojojin na Sama da na Kasa da na Ruwa da shugabannin Yansanda su ka halar ta amma a ka dage zaman. Ya ce dalilin da ya sa a ka da ge ganawa da Shugabannin tsaron shi ne domin a bawa dukkannin ma su ruwa da tsaki da ma su bayar da gudunmawar su wajen maganta matsalar tsaro da ta addabi wannan kasa.

Sanata Hussaini, ya ce Majalisa ta lura da cewa an saba shirya irin wannan zama amma ba’a cika samun biyan bukata ba sabo da haka ne su ka ga dacewa na gaiyatar dukkanin Shugabannin tsaro ma su mulki da ma su aiwatarwa aiki domin a hada su a guri guda don lalubo mafita mai dorewa.

Ya ce sabo da haka ne ya sa a ka dage zaman domin ya bawa Ministan Tsaro, Badaru Abubakar da Mai bawa Shugaban Kasa Shawara akan Harkar Tsaro, Nuhu Ribado da ma da su halarci wannan zama don magance matsalar tsaron baki daya.

A wani bangare kuma, Sanatan ya goyi bayan shawarar da wata Kungiya ta bayar na yin amfani da Sarakuna wajen magance matsalar tsaro da ta addabi kasarnan. In da ya ce a matsayin sa na basarake ya san irin gudunmawar da Sarakuna su ke bayarwa wajen samar da zaman lafiya tun lokacin Turawa wanda ya ce hakan ne ta sa su ka yi amfani da su wajen Mulkin Mallaka a Arewacin Najeriya.

Kungiyarnan Mai Rajin Samar Da Yanayi Na Zaman Lafiya (CEPEJ), ta bukaci Gwamnati da ta yi amfani da shugabannin gargajiya wajen samar da tsaro a Kasarnan a matsayin su na iyayen kasa kuma ma su kula da al’adu.

IMG 20240208 WA0088

Shugaban Kungiyar, Komared Sheriff Mulade wanda ya yi wani taro na Yanjarida in da ya nu na irin mahimmancin Sarakuna da rawar da su ke takawa wajen samar da zaman lafiya da bunkasa al’adu ya bukaci Gwamnati da ta ja sarakuna a jiki domin su tallafa mata wajen maganta matsalar tsaro da ta addabi kasarnan.

Da ga karshe ya yi kira ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da kada ya sassauta wajen daukar zafafan matakai na magance matsalar tsaro da ta addabi Kasarnan ganin yadda barazanar ta ke neman ta wargaza kasancewar kasarnan a matsayi kasa daya al’umma daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here