Home Siyasa Majalisar Dattawa Za Ta Cigaba Da Tantance Ministoci 19 Ranar Juma’a

Majalisar Dattawa Za Ta Cigaba Da Tantance Ministoci 19 Ranar Juma’a

149
0
Senate President Akpabio

Majalisar Dattawa ta ce za ta fara tantance sabbin sunayen Ministoci  guda 19 da Fadar Shugaban Kasa ta mika mata yau Alhamis ranar Juma’a inji Shugaban Majalisar Godswill Akpabio.

Ya yin da ya ke karanta jerin sunayen wadanda Shugaban Kasar Bola Ahmad Tinubu ya turo Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Kasa, Femi Bajabiamila da kan sa ya kai sunayen da yammacin Laraba kamar yadda ya kawo na farko.

Bayan da Majalisar ta gama tantance mutane 28 da Shugaban Kasar ya aiko da su da fari a yau Laraba sai Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya sanarwa yan uwansa yan Majalisar wasikar da Shugaban Kasar ya aiko da ita da jerin sunayen Ministoci 19, wanda jimillar su ya kai 47 kamar haka:

 1. Abubakar Momoh – Edo
 2. Betta Edu – Kuros Riba
 3. Uche Nnaji – Enugu
 4. Joseph Utsev – Binuwai
 5. Hannatu Musawa – Katsina
 6. Nkeiruka Chidubem Onyejocha – Abiya
 7. Stella Okotete – Delta
 8. Uju Kennedy-Ohanenye – Anambra
 9. Ahmed Dangiwa – Katsina
 10. Olawale Edun – Ogun
 11. Imaan Suleman Ibrahim – Nasarawa
 12. Bello Muhammad Goronyo – Sokoto
 13. Nyesom Wike – Ribas
 14. David Umahi – Ebonyi
 15. Mohammad Badaru Abubakar – Jigawa
 16. Nasir El-rufa’i – Kaduna
 17. Lateef Fagbemi – Kwara
 18. Doris Aniche Uzoka – Imo
 19. Yusuf Maitama Tuggar – Bauchi
 20. Farfesa Ali Pate – Bauchi
 21. Ekerikpe Ekpo – Akwa Ibom
 22. Sani Abubakar Ɗanladi – Taraba
 23. Mohammed Idris – Neja
 24. Olubunmi Tunji Ojo – Ondo
 25. Dele Alake – Ekiti
 26. Waheed Adebayo Adelabu – Oyo
 27. John Eno – Kuros Riba
 28. Abubakar Kyari – Borno
 29. Abdullahi Tijjani Gwarzo – Kano
 30. Maryam Shetti – Kano
 31. Ishak Salako – Ogun
 32. Bosun Tijjani – Ogun
 33. Tunji Alausa – Legas
 34. Tanko Sununu – Kebbi
 35. Adegboyega Oyetola – Osun
 36. Atiku Bagudu – Kebbi
 37. Bello Matawalle – Zamfara
 38. Ibrahim Geidam – Yobe
 39. Simon Lalong – Filato
 40. Lola Adejo – Legas
 41. Shuaibu Abubakar – Kogi
 42. Tahir Mamman – Adamawa
 43. Aliyu Sabi Abdullahi – Neja
 44. Alkali Ahmed Saidu – Gombe
 45. Heneken Lakpobiri – Bayelsa
 46. Uba Maigari – Taraba
 47. Zephaniah Jissalo – Abuja

Tuni Majalisar ta umarci wadanda aka turo da sunayen na su da su je su bayar da bayanen su gobe Alhamis domin yin hakan shi ne zai bayar da damar a fara tantance su ranar Juma’a.

Domin hakan ya tabbata, Majalisar ta bawa kanta hutu na kwana daya wato gobe Alhamis domin ya bata dama ta dawo ranar Juma’a don ta fara tantance jerin Ministocin da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya aike mata da su.

Ga dukkan alamu, tantance Ministocin zai saka Majalisar ta cigaba da zamanta har zuwa ranar Asabar domin ta samu ta tantance su. Bayan Majalisar ta tantance su, akwai bukatar ta sake zama domin amincewa ko akasin haka, wato dai ga dukkan alamu Majalisar zata ci gaba da zama ranar Litinin domin amincewa da Ministocin.

Da zarar Majalisar ta gama amincewa da Ministoci, za ta aikewa da Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu rahoton aikin da ta gudanar. Idan har ta ki amincewa da wani da ga cikin sunayen da ya gabatar za ta ba shi shawara na abun da ya kamata ya yi wato ya sake kawo sunan wasu domin su chanji wanda suka ki tantacewa da su..

Shi kuma Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu da zarar ya karbi sunayen wadanda aka amince da tantance su zai sanar da su ma’aikatun da ya ke so su yi aiki, Kuma ba tare da bata lokaci ba za a rantsar da su a babban dakin taro na Fadar Shugaban Kasar domin su je su kama aiki ba tare da bata lokaci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here