Home Uncategorized Majalisar Dattawa Tace An Sace Kudade A Lalitar Gwamnatin Taraiya Kimanin Naira...

Majalisar Dattawa Tace An Sace Kudade A Lalitar Gwamnatin Taraiya Kimanin Naira Tiriliyan Daya Da Ga 2015 Zuwa 2019

214
0

Majalisar Dattijai tace ta gano cewa an sace kudade a lalitar Gwamnatin Taraiya kimanin naira Tiriliyan daya daga shekara ta 2015 zuwa yanzu da ga ma’aikatu daban daban na Gwamnatin Tariaya dake kasarnan.

Shugaban Kwamitin Bincike na Majalisar Dattijai, Sanator Ibrahim Hadejia ne ya sanar da haka a hirar sa da Jaridu harda Viewfinder a Majalisar Tariya da ke Abuja.

Sanata Hadejia yace Kwamitinsa ya na shawartar Gwamnatiin Taraiya da ta yi amfani da rahoton kwamitin Binciken kudi wanda suka gabatar a wata hanya daya tilo da ka iya dakile cinhanci da rashawa a kasarnan.

Yace, binciken su ya gano cewa yaki da cinhanci da rashawa da akeyi, ana barin jaki ne ana dukan taiki. “ a maimakon a hana cinhanci da rashawa a kasarnan, sai a bari mutum yaci hancin sannan daga baya ace wai za’a hukun ta shi.

Sanata Hadejia yace, abun da ya kamata a yi shine a karfafi ofishin Mai Binciken Kudi na Gwamnatin Taraiya wato Akanta Janar kamar yadda yake a sauran kasashen duniya a mai makon kafa hukumomi da sai anyi cinhancin sannan su kama mutum.

Yace, rahoton da suka gabatarwa Gwamnatin Taraiya na shekaru hudu ya bayar da shawarwari na yadda za’a dakile cinhanci da rashawa a ma’aikatu na Gwamnatin Taraiya ta hanyar hana ma’aikatan satar kudin gwamnati a maimakon a barsu suyi satar sannan a ce wai za’a hukuntasu.

Hadejia yace, bashin da ake bin kasarnan na kusan naira Tiriliyan Tamanin, za a biyan kudin idan an toshe hanyoyi da ake bi wajen satar kudin kasarnan ta hanyoyi da dama kamar biyan kudin tallafin Mai da yadda bankin Gwamnatin Taraiya yake baiwa wasu shafaffu da mai Dala Amurka a farshin gwamnati su sayar da ita a farashin bayan fage da sauran hanyoyi da dama.

Ya bukaci cewa idan da gaske akeyi za a yaki cinhanci da rashawa  a kasarnan toh ya zama dole a karfafi Ofishin Akanta Janar domin ya gudanar da aikin sa kamar yadda doka ta tanadar.

Har ila yau, ya bukaci ita kanta Majalisar Taraiya data yi doka da zata karfafi Ofishin Akanta Janar ta yadda shine zai rinka daukar Ma’aikatansa ba wai a dauka masa ba, sannan a bashi cin gashin kansa ta yadda baza ayi masa katsalandan ba wajen gudanar da aikin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here