Home Siyasa Majalisar Dattawa Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Aka Jinginar Da Tashar...

Majalisar Dattawa Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Aka Jinginar Da Tashar Jirgin Sama Ta Malam Aminu Kano, Tare Da Alkawarin Daukar Mataki

183
0
SEN. Kawu

Majalisar Dattawa ta yi Allah wadai da yadda aka Jinginar da Tashar Jirgin Sama ta Malam Aminu Kano da ke Kano tare da yin kira ga Gwamnatin Taraiya da ta gaggauta janye wannan jinginarwa har sai anyi bincike akanta.

Majalisar ta yi wannan Allah wadai ne yau Alhamis a zauren Majalisar Dattawa a yayin da Sanata Mai  Wakiltar  Kano ta Kudu, Sanata Kawu Sumaila ya gabatar da Kudurin gaggawa a gaban Majalisar.

Majalisar ta amince da biyu da ga cikin bukatu uku da Sanatan ya yi na cewa a binciki yadda aka bayar da jinginar da Tashar Jirgin  Saman na Kano tare da yin kira ga Gwamnatin Taraiya da ta bawa masu sha’awar jinginar tashar dama suma su shiga a dama da su.

Majalisar ta ce ba laifi bane jinginar da tashar Jirgin Saman sai dai ba a yi shi ba a lokacin da ya dace kuma an karya dokoki wajen aiwatar da jinginarwar.

Majalisar Dattawan ta ce an bayar da wannan Kwangila ne ranar 17 ga watan Mayu na shekara ta 2023, wato yan kwanaki kadan suka ragewa Gwamnatin da ta sauka da ga kan mulki.  Kuma wa’adin da aka daukawa kamfanin da aka bawa kwangilar wato “ Messrs Corporacién America Airports Consortium” shekaru 30 sun yi yawa.

Sanata Kawu Sumaila wanda shine ya gabatar da Kudurin ya yi Karin bayani ga yan jaridu a wata hira da shi bayan da Majalisar ta amince da bukatun na sa in da ya ce kudade da aka ce kamfanin zai rinka biya sunyi mutukar kadan na Dalar Amurka Miliyan daya da rabi ($1.5m) bayan kuma tashar Jirgin saman ta na iya samar da kudin shiga kimanin Dalar Amurka Miliyan 97.4 a shekara.

Sanata Sumaila ya ce akwai rainin hankali da son zuciya a wannan jinginarwa shine dalilin da ya sa ya gabatar da wannan kuduri domin ya kwatowa mutanen Kano hakkin su.

Ya ce a hakikanin gaskiya ma ofishin Ministan Zirga Zirgan Jiragen Sama bashi da iko na Jinginartar da Tashar. Hukumar kula da Jiragen Sama ta Kasa wato FAAN ita ce ke da iko wajen jinginantar da Tashar.

Majalisar Dattawan ta nu na bacin ranta wajen ganin yadda aka gudanar da jinginar da Tashar tare da yin alkawarin kafa wani Kwamiti na Musamman domin ya bibiyi dukkanin Jiginarwar da aka yiwa Tashoshin Jiragen Saman Kasar nan da zarar sun kafa Kwamitoci dake da alhakin yin hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here