Home Uncategorized Majalisar Dattawa Ta Yaba Kwarewa Ta Yan Jaridun Fadar Majalisa Ta 9

Majalisar Dattawa Ta Yaba Kwarewa Ta Yan Jaridun Fadar Majalisa Ta 9

174
0

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya yabawa Yan jarida masu kawo rahoto daga Majalisar Dattawa game da kokarin da suke yi na aiwatar da aiyukan na fadakar da Yan Najeriya rahotanni na gaskiya cikin kwarewa da sanin ya kamata.

Shugaban yayi wannan bayani ne a lokacin da yake yin bankwana da Yan jaridun a matsayinsa na Shugaban Majalisar Dattawa ta Tara a daya daga cikin dakin taron Majalisar a jiya Laraba.

Ahmad Lawan  yace a shekaru sama da ashirin da yayi a Majalisar ya gamsu cewa wadannan Yanjaridu na Majalisar ta Tara sune suka fi duk wasu Yanjaridu kwarewa da sanin makamar aiki da nuna sanin ya kamata wajen gudanar da aiyukan su.

Yace nasara da gwamnatinsa ta samu na alaka da irin kyakkyawar dangantaka da Yan jaridun. Kuma sunyi nasarori da yawa a inda yace tunda akayi Majalsiar ba’a samu Majalisa tayi  Kuduri masu yawa kamar tasu ba.

Inda yace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sakawa Kudurai 112 hannu indan aka kwatanta da kudure kudure 75 da sauran Shugabanni da sukayi a Majalisu da suka gabata.

Shugaban Majalisar Dattawan ya kara da cewa ya lura cewa wasu daga cikin yan Jaridun sun kasance tare da Majalisar tunda yazo a shekara ta 1999 sabo da haka akwai kwarewa da sanin makamar aiki tare da dasu.

Sanata Ahmad Lawan ya godewa Yan jaridun irin hadin kai da suka bashi wajen sanar da Yan Najeriya irin aikace aikace da Majalisa ta Tara tayi. Wanda tun da aka fara Majalisar a shekara tao 1999 ba’a taba samun wata Majalisa tada ta yi aiki kamar Majalisa ta 9 ba.

Shugaban Yan Jaridun, Jame Itodo ya godewa Shugaban Majalisar Dattawan Ahmad Lawan na irin hadin kai da ya bawa Yanjaridun wanda yace hakanne ya kawo zaman lafia tsakanin Majalisar Ta Tara da Yan Jaridun.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here