Home Ilimi Majalisar Dattawa Ta Umarci Gwamnatin Taraiya Da Ta Gaggauta Kammala Gina Kwalejin...

Majalisar Dattawa Ta Umarci Gwamnatin Taraiya Da Ta Gaggauta Kammala Gina Kwalejin Horas Da Jami’an Hana Fasa Kwauri Ta Kasa Da Ke Bauchi

166
0
Sen. Buba, Bauchi

Majalisar Dattawa ta umarci Gwamnatin Taraiya da ta gaggauta  ganin an kammala gina Makaratar Horas da Jami’an Hana Fasakwauri ta Kasa wato Kwastom dake Jihar Bauchi don inganta samar da jami’ai kwararru da za su kawo gyara da cigaba a kasarnan.

Majalisar ta bayar da wannan umarni ne ran Alhamis a lokacin da Sanata Mai Wakiltar Bauchi ta Kudu, Sanata Buba Umar Shehu ya gabatar da bukata ta musamman a gaban Majalisar.

Sanata Buba ya ce dalilin gabatar da wannan kuduri shine ya lura cewa an saka ginin wannan makaranta a cikin kasafin Kudi na shekara ta 2023 in da za a kashe kimanin kudi sama  da Naira Biliyan 14 amma har ya zuwa yanzu shekara ta raba ba a yi komai akan gina makarantar ba.

Ya ce gina wannan makaranta zai kawo gagaramin cigaba ga kasa baki daya ta hanyar samar da horo ga jami’an Hana Fasa Kwauri wanda zaiyi sanadiyar kawo cigaba ta fannin samar da kudin shiga da kwarewa da kawar da barna a gurare da dama a kasarnan.

Kudurin nasa wanda ya sami goyan bayan dukkanin Sanatocin Majalisar in da suka bayar da gudunmawa wajen ganin anja hankalin gwamnatin Taraiya ta gaggauta ganin an samar da makarantar don amfanar Yan Najeriya.

Sanata Buba ya ce yana da kwarin gwiwa cewa Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai bayar da umarni ba tare da bata lokaci ba wajen ganin an kammala makarantar sabo da muhimmancin ta ga kasa ta fannin tsaro da samar da kudaden shiga.

A wani bangaren kuma, Sanata Buba ya sha alwashin ganin an samar da ingantaccen tsaro a kasarnan ta hanyar tattaunawa da jami’an tsaro akai akai a matsayin sa na shugaban Kwamitin da aka kafa a Majalisar akan fannin Tsaro.

Ya ce tsaro shine ginshikin duk wani cigaba sabo da haka ne bazaiyi kasa a gwiwa ba wajen ganin an samar da ingantaccen tsaro a kasarnan.

A hirarsa da Yan Jaridu a ofishinsa, Sanata Buba ya yi kira da Yan Najeriya da su bawa Jami’an tsaro hadin kai wajen ganin an samar da tsaro mai inganci a kasarnan. In da ya kara da cewa hakki ne da ya dogara akan kowo tun da ba wanda zai magance mana barazanar tsaro a kasarnan sai mu da kammu mun hada gwiwa da jami’an tsaro.

A bangaren Ministoci da aka gabatar da sunayen su yau Alhamis, ya yabawa kokarin Shugaban Kasa na ganin ya gabatar da sunayen kamar yadda kundin tsarin mulki ya bukata.

Da ga karshe ya yi kira da Yan Najeriya musamman wadanda ba a fadi sunayen Ministoci da ke Jihohin su ba da su kara hakuri cewa Shugaban kasa ya yi alkawari gabatar da sauran sunayen watakila kafin a gama tantance sunayen wadanda aka gabatar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here