Home Kotu da 'Yan sanda Majalisar Dattawa Ta Sha Alwashin Yin Doka Mai Tsanani Akan Wanda Aka...

Majalisar Dattawa Ta Sha Alwashin Yin Doka Mai Tsanani Akan Wanda Aka Samu Da Aikata Fyade

205
0
Sen. Kingibe

Majalisar Dattawa ta sha alwashin yin dokoki ma su tsanani akan duk wanda aka samu da yiwa mata da kananan ya yara fyade a wani mataki na dakatar da wannan mummunan dabi’a a Najeriya.

Majalisar ta dauki wannan mataki ne lokacin da Sanata Mai Wakiltar Birnin Taraiya Abuja, kuma Shugaban Kwamitin Mata, Ireti Heebah Kingibe ta gabatar da Kuduri na gaggawa a gaban Majalisar yau Alhamis.

Sanata Kingibe ta ce dalilin gabatar da wannan kuduri shi ne domin ta ja hankalin mambobin Majalisar akan wannan mummunan dabi’a a wani mataki na wayar da kansu akan irin illar da take tattare da wannan dabi’a da ta ke neman ta gagari kwandila.

Ta ce Majalisar Dinkin Duniya ce ta ware ranaku 16 da ya kamata ayi amfani da su wajen gaggamin wayar da kan jama’a akan illar wannan dabi’a.

Sanatan ta nuna takaicin ta na yadda ake samun karuwar fyade a kasarnan. “wannnan dabi’a ta yi muni kwarai da gaske in da an sami uba ya yiwa yar sa fyade, an yiwa yar wata bakwai fyade da yar shekara daya, wannan abu ya yi mu ni kwarai”. In ji ta.

Kingibe ta ce dalilin da ya sa ta kenan ta gabatar da wannan kuduri a gaban Majalisar domin a karfafa dokar fyade ta yadda mai aikata wannan dabi’a zai yi nazari da kyau kafin ya aikata sa bo da tsananin dokar.

Ta kara da cewa ba zai zama laifi ba idan aka daure wanda ya yi fyade shekaru 20 a gidan yari ko ma a yanke masa hukuncin kisa sabo da girman laifin da ya aikata.

Sanata Kingibe ta ce ta ji dadi da yadda dukkan Yan Majalisar su ka nuna goyon bayan su akan Kudurin da ta gabatar kuma Majalisar ta amince da dukkan bukatun da ta gabatar wanda hakan na nufin za ta kara sabun ta Dokar Fyade a Najeriya.

Shugaban Kwamitin Matan ta roki jami’an tsaro da su bawa wannan yunkuri na su hadin kai da goyon baya ta hanyar kara saka ido da kama duk wanda aka kama da wannan dabi’a kuma a gabatar da shi a koto domin ya fuskanci hukunci mai tsauri.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here