Home Siyasa Majalisar Dattawa Ta Sha Alwashin Samar Da Wadatattun Kudade Don Inganta Titunan...

Majalisar Dattawa Ta Sha Alwashin Samar Da Wadatattun Kudade Don Inganta Titunan Najeriya

93
0
Sen. Hussaini

Majalisar Dattawa ta sha alwashin ganin cewa titunan Najeriya wadanda suke karkashin Gwamnatin Taraiya kimanin kilomita 38,000 sun sami wadacecen kudaden gudanarwa wanda za su inganta titunan domin jin dadin zirga zirgan Yan Najeriya.

Shugaban Kwamitin da ya ke kula da Hukumar da ta ke kula da Titunan Najeriya wato FERMA, Sanata Babangida Hussaini, dan Majalisar Datttawa da ke Wakiltar Jigawa ta Arewa maso Yamma ne ya baiyana haka ga Yan jaridu a ofishin sa da ke Majalisar Taraiya a Abuja ranar Talata.

Sanata Hussaini, wanda Kwamitinsa ya tantance shugabannin gudanarwa na Hukumar ya ce sun gamsu da irin bayanai da mambobobin kwamitin su ka gabatar mu su na irin kudure kuduren da suka tanada na ganin sun inganta titunan Najeriya.

Sabo da haka Sanatan ya ce Majalisar Dattawa zata yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta samar da wadatattun kudade a kasafin kudi na shekara ta 2024 domin ganin an inganta titunan Najeriya.

Sanata Hussaini ya kara da cewa ingantattun tituna sune kashin bayan kawo cigaban arzikin kasa da yan kasa sabo da haka Kwamitinsa za ta saka ido wajen ganin an gina titunan masu inganci don cigaban Najeriya.

Har ila yau, ya ce kyawawan tituna suna da alaka da yalwatar arziki da samar da tsaro mai inganci domin masu laifi su na amfani da tituna marasa kyau wajen yin fashi da ta’addanci iri – iri a Najeriya. Sa bo da haka, kwamitin sa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an aiwatar da tituna masu inganci.

Sanatan ya kuma karyata zargin da ake yi na cewa Hukumar FERMA tana gudanar da aiyuka akan tituna da aka bayar da kwangilar su. In da ya yi karin haske cewa a kowacce kwangila ana ware wasu kudade domin gyara titunan da suka fashe kafin aiki ya zo kansu don matafiya su sami saukin tafiya.

In da ya bayar da misali da titun Abuja zuwa Kaduna ya ce kwamitin sa ya umarci kamfanin da ya ke kwangilar sake gina titin da ya cike ramuka a gurare da dama kamar gadar Rijana da wurin juyawa da ke Jere da sauran ramuka sabo da akwai kudade da ake warewa domin yin hakan.

Da ga karshe Sanata Babangida Hussaini ya roki Yan Najeriya da su rinka bawa gwamnati da kamfanoni da aka bawa kwangila hadin kai wajen bin doka da tsare tsare na gudanar da aikin don samun ingantattun tituna da za a dade ana morar su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here