Home Zirga zirga Majalisar Dattawa Ta Sha Alwashin Ganin An Kammala Titin Abuja Zuwa Kaduna...

Majalisar Dattawa Ta Sha Alwashin Ganin An Kammala Titin Abuja Zuwa Kaduna Nan Bada Dadewa Ba

155
0
Sen. Lar

Majalisar Dattawa ta sha alwashin duk yin mai yuwuwa ta ga an kammala titin mota da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna cikin dan kankanin lokaci.

A wani kuduri na gaggawa da Sanata Mai Wakiltar Kaduna ta Tsakiya ya gabatar, Sanata Adamu Usman  – Mr. Lar ya bukaci da Majalisar da ta gaiyaci kamfanin da ya ke gudanar da aikin titin don jin dalilin da ya sa aikin ya ke tafiyar wahainiya.

Lar ya ce batum rashin tsaro a hanyar yanzu ya zama tarihi sabo da haka baiga dalilin da ya sa aikin baya tafiya kamar yadda ya kamata ba. Ya ce ko da yake a baya yasan rashin tsaro a hanyar ya sa an dakatar da aikin amma kusan sama da shekara guda kenan an samu saukin rashin tsaro a kan hanyar.

Sanatar Lar ya ce aiyuka guda uku masu mahimmanci gwamnatin da ta shude ta bayar wato 2nd Niger Bridge da Titin Lagos zuwa Ibadan da kuma Abuja zuwa Kano amma abun takaici an gama biyu da ga Kudu, amma daya da ga Arewa ya gagara.

Sabo da haka ya ce da zarar an kammala kafa kwamitoci, kwamitin aiyuka zai gaiyaci Kamfanin da yake aikin da Ma’aikatar Aiyuka ta Gwamnatin Taraiya dama Ma’aikatar kudi domin jin ina ne Gizo ya ke saka.

Sanata Lar a hirar sa da Yan Jaridu ya jaddada muhimmancin titin Abuja zuwa Kaduna, zuwa Kano; in da ya ce ko da yake an kusa kammala  zuwa Kano amma da ga Kaduna zuwa Abuja akwai bukatar a hanzarta gudanar da aikin titin.

Ya ce an rasa rayuka da dukiyoyi masu yawa sakamakon rashin kyan titin sabo da haka Majalisar ta 10 ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta saka idon don ganin an kammala aikin titin nan ba da dadewa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here