Home Zirga zirga Majalisar Dattawa Ta Haramta Tashoshin Mota Barkatai A Abuja

Majalisar Dattawa Ta Haramta Tashoshin Mota Barkatai A Abuja

161
0
Sen. Wadada

Majalisar Dattawa ta yi kira ga Hukumomin Babban Birnin Taraiya Abuja wadanda suka hada da FCTA da VIO da FRSC da AEPB da sauran masu ruwa da tsaki akan harkar Sufuri da su gaggauta dakatar da Tashoshin Mota wadanda suke ba a kan ka’ida ba a birnin.

Majalisar ta bayar da wannan umarni ne ranar Alhamis bayan da Sanata Mai Wakiltar Jihar Nasarawa ta Yamma, Aliyu Ahmad Wadada ya gabatar da Kuduri na gaggawa wanda ya bukaci da a dakatar da tashoshi wadanda suke ba a kan ka’ida bad a suka mamaye birinin.

Majalisar har ila yau ta amincewa wadannan hukumomi das u dauki matakai masu tsauri na cin tara ga duk wanda aka kama yana gudanar da hayar mota a tasha da suke ba bisa ka’ida ba.

Sanata Wadada ya yi wa Yan Jaridu Karin haske akan wannan kuduri da ya gabatar in day a ce dalilinsa na kawo wannan kuduri shine; ya lura cewa tashoshin mota wadanda ba bisa ka’ida ba sun yi yawa a birnin Abuja kuma yadda ko’ina ya zama tashar mota.

Wadada y ace wannan ya sabawa tsarin da aka yiwa birnin kuma hakan barazana ne ga tsaro da lafiya da kuma zamantakewa na mazauna birnin. Bayan haka ya wargaza kyakkyawan tsari da akayi na cewa ya zama birnin mafi kyawu a Africa.

Sanatan ya kara da cewa bayan haka, aikace-aikace irin su kasuwanci da tsafta na birnin da cunkoso ya kasance ba bisa ka’ida ba. Wannan ya saka birnin ya yi muni da yawa.

Sabo da haka ya ce Majlisa ta gomo ta kuduri aniyar tabbatar da cewa zata dawo wad a birnin martabarsa kamar yadda aka tsara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here