Home Kwadago Majalisar Dattawa Ta Cire Yan sanda Daga Cikin Tsarin Fansho Na Pencom

Majalisar Dattawa Ta Cire Yan sanda Daga Cikin Tsarin Fansho Na Pencom

207
0

Sakamokon korafe korafe da Yan sanda ke yi game da tsarin Fansho na Kasa wato Pencom Majalisar Dattawa ta cire Yan sanda da ga cikin tsarin bayan ta gamsu da korafe korafen nasu.

Majlisar Dattawan ta amince da wannan bukata ne yau Talata bayan kwamitin da aka baiwa alhakin tantance bukatun na su Karkashin Shugabancin Sanata  Halliru Dauda Jika, mai wakiltar Bauchi ta tsakiya ya gabatar da rahoton sa a gaban Majalisar.

Majalisar Dattawa ta karbi rahoton kwamatin na ta mai kula da harkokin ‘Yansanda, inda ya bayar da shawarwarin da suka kamata Kan batun Kafa Hukumar kula da Fanshon jami’an ‘Yansanda.

 

Da ya ke gabatar da rahoton kwamatin a zauran majalisar Sanata Jika ya jaddada cewa wannan mahimmin aiki ne domin ceto jamian da  ga shiga cikin matsalolin da bai kamata ba bayan kammala aikin kare jamaa.

 

Sanata Jika ya kara da cewa Yansanda su suka fi cancanta na a cire su da ga cikin wannan tsarin na Pencom ganin cewa tuni Sojoji da sauran masu kayan kaki sun fita da ga cikin tsarin.

 

Ya ce sun so su cire Yansandan tuntuni da ga cikin tsarin amma sai sukayi karatun ta nutsu wajen ganin an yi abun da ya kamata na yin tsare tsare da zasu kare martabar Dan sanda wanda aikin sa shine ya kare ruyuka da dukiyoyin al’umma.

 

Sanata Jika ya kara da cewa kwamitinsa ya bayar da shawarwari da suka dace na ganin an kare martabar Dan sanda. Abun da ya rage shine Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu ya saka hannu domin Kudurin ya zama doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here