Home Siyasa Majalisa Taraiya Ta 9 Ta Ciri Tuta Inji Sanata Barkiya

Majalisa Taraiya Ta 9 Ta Ciri Tuta Inji Sanata Barkiya

183
0

An baiyana Majalisa ta tara a matsayin Majalisa wacce tayi fice wajen gabatar da kudure kudure mafi yawa tun lokacin da aka sami dorewa demokradiyy a Najeriya shekaru 22 da suka gabata.

Sanata Kabiru  Abdullahi Barkiya Dan Majalisa mai wakiltar Katsina ta tsakiya ne ya sanar da haka a hirarsa da Yanjaridu a ofishinsa dake Majalisar Dattawa a Jiya Alhamis.

Ya ce da ga cikin kudure kudure da Majalisar ta samu nasarar yi musu doka da da zasu kawo cigaba ga Najeriya sun hada da Kudurin Mai da dangoginsa wato “PIB Bill” da gyara akan Kudurin Tsarain Mulki da Kuma Kudurin Gudunar da Zabe.

Sanata Barkiya yace wadannan kudure kudure sun gagari Kwandila tun 1999 amma cikin yardar Allah Majalisa ta 9 tayi nasarar yi masu doka kuma Shugaban Kasa ya sakawa dokokin hannu.

Ya ce shima a karan kansa ya yi nasarar gabatar da kudure kudure har guda 4 sabo da haka ya na fatan shugaban Kasa Bola Ahman Tinubu ya saka masu hannu su zama doka don anfanin yan Najeriya.

Sanatan ya yabawa tsohuwar gwamnati wajen kokarin da ta yi a bangaren Tsaro inda ya nemi wannan gwamnati data dora a inda aka tsaya. Inda yace yin hakan zai kawo gagarumin cigaba ga kasarnan.

Bayan haka Sanata Barkiya ya shawarci Shugaban Kasa Ahmad Bola Tinubu da ya farfado da masana’antu musamman a Arewa kamar masana’antun samar da ya dudduka da sauransa.

Ya ce hakan zai kawo cigaba ta hanyar dakile zaman banza ga samari tare da bunkasa tattalin arzikin kasa kuma zai tallafa wajen magance rashin tsaro a kasarnan.

Daga karshe Sanata Barkiya ya yi kira ga Yan Najeriya das u bawa gwamnatin Bola Ahmad Tinubu goyon baya tare da yi mata addu’a domin ta sami damar warware matsaloli da suka addabi kasarnan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here