Home Siyasa Magoya bayan PDP na zanga-zanga kan dambarwar zaɓen Adamawa

Magoya bayan PDP na zanga-zanga kan dambarwar zaɓen Adamawa

211
0

Magoya bayan jam’iyyar PDP a Adamawa sun shiga kwana na biyu na zanga-zanga a Yola, babban birnin jihar yayin da ake ci gaba da dambarwa a kan zaɓen gwamna da aka kammala ranar Asabar.

Ɗaruruwan magoya bayan Gwamna Ahmadu Fintiri ne suka yi maci daga hedkwatar PDP zuwa ofishin hukumar zabe, inda suke rera taken nuna goyon baya ga gwamnan mai ci da kuma buƙatar a koma don ci gaba da tattara sakamakon zaɓen.

An kammala zaɓen gwamnan jihar ne ranar Asabar ɗin da ta wuce, sai dai aikin tattara sakamakon zaɓen ya shiga ruɗani bayan kwamishinan zaɓen jihar ya sanar da Aisha Dahiru Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen, duk da yake ba a kammala aikin tattara sakamakon ba.

Hedkwatar INEC da ke Abuja ta fitar da wata sanarwa, inda ta ayyana matakin kwamishinan zaɓen nata a matsayin haramtacce, kuma ta dakatar da aikin tattara sakamakon.

Washe gari kuma INEC ta sanar da dakatar da kwamishinan zaɓen jihar, Barrister Hudu Ari daga aiki.

Ba a dai san hakikanin yaushe za a koma don ci gaba da tattara sakamakon zaɓen ba, da kuma sanar da wanda ya yi nasara. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here