Home Kotu da 'Yan sanda Ma’aikaciyar jinya ce babbar abar zargi kan mutuwar Mohbad – Ƴan sanda

Ma’aikaciyar jinya ce babbar abar zargi kan mutuwar Mohbad – Ƴan sanda

166
0
Mohbad

Rundunar ƴan sanda a jihar Legos ta yi karin haske a kan binciken da take yi a kan mutuwar mawakin Najeriyar nan, Ilerioluwa Aloba wanda aka fi sani da suna Mohbad.

Yayin wani taron manema labarai da ta gabatar a hedikwatarta da ke Ikeja a birnin Lagos, kwamishinan ‘yan sanda a jihar, CP Idowu Owohunwa ya ce marigayin ya fara barkewa da amai sannan sai tsigar jikinsa ta rika tashi bayan wata ma’aikaciyar jinya ta yi masa allura har sau uku.

Ya ce ma’aikaciyar jinyar Feyisayo Ogedemgbe ta yi wa Mohbad allurorin ne ranar 12 ga watan Satumban 2023.

Taron dai a cewar Kwamishinan ‘Yan sanda Idowu Owohunwa, kokari ne na bayar da bayanai a kan rahotannin farko-farko a kan binciken da ‘yan sanda suke yi don bankado abubuwan da suka kai ga mutuwar Mohbad.

Ya kara da cewa ya zuwa yau Juma’a, ‘yan sanda sun yi wa jimillar shaidu guda 26 tambayoyi.

Kwamishinan ‘yan sandan Lagos ya ce a cikin wadanda ‘yan sanda suka yi wa tambayoyi har da mahaifin Mohbad da mahaifiyarsa da kanwarsa da dan’uwansa da matarsa da manajansa.

Ya ce an kai Mohbad asibiti be bayan ya rasu, kuma likitocin da ke aiki suka ba da tabbacin mutuwarsa ranar 12 ga watan Satumba.

Ma’aikaciyar jinyar Feyisayo Ogedemgbe, in ji Idowu Owohunwa, wadda abokin Mohbad, Ayobami Sodiq da aka fi sani da Spending, ya sanya, ta yi wa mawakin allurori a gidansa, wadanda aka yi imani sun haddasa sanadin da ya kai ga mutuwar mawakin. (BBC).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here