Home Siyasa Lallai Za Muyi Gyara A Shugabancin Kungiyar Sanatocin Arewa – Inji Sanata...

Lallai Za Muyi Gyara A Shugabancin Kungiyar Sanatocin Arewa – Inji Sanata Sani Musa

156
0
20231003 164345

Shugaban Kwamitin Kudi na Majalisar Datttawa, Sanata Sani Musa ya ce  ya zama wajibi a yi gyara a yadda a ke tafiyar da Kungiyar Sanatocin Arewacin Kasarnan.

Ya fadi haka jimkadan bayan da  Majalisar Datttawa ta dakatar da Shugaban Kungiyar, Sanata Abdul Ningi wanda ta ce ya yi mata kage na yin cushe a cikin kasafin kudi na 2024 a hirarsa da Yan Jaridu a ofishin sa.
Sani Musa ya ce yadda a ke jagorancin Kungiyar a na fifita wasu yan Kungiyar fiye da wasu sabo da yankin Arewacin da su ka fito.
” Arewar daban-daban mu ke. Ku yan arewan ku na dubawa cewa mutum da ya fito da ga North West ko North East shi ne dan Arewa, mu yan North Central ba yan Arewa ba ne. Wannan a bu ya kamata a gyara.
“Lallai zamuyi gyara, so sai za muyi gyara.  Idan kuka duba yadda aka zabi Shugabanci na Kungiyar ai mun duba ba a rabata dadai ba. Ku na da rinjaye ku dauki Shugabancin ku, ku bawa maras rinjaye.  Wanda zai ce ko kun yi mai kyau zai ce bakuyi mai kyau ba. Yan adawa mana. Lallai za mu yi gyara.”
Sanata Musa ya cigaba da cewa maganar hadin kai ita ce idan kaga daidai ka bi, idan kuma a ka ce ga hanyar da zamu bi gabadaya a bi, idan aka ce a bari sai a bari. Amma ni ina da sanin cewa in ka buda bakinka ka ce za kai abu, ko ba za kai abu ba, bai kamata kayi abu ba bayan ka ce ba za kai ba.”
Sanatan ya ce dakatar da Sanata Abdul Ningi gyara kayan ka ne, domin a dukkan Majalisar babu wanda ya ke fada da Sanata Ningi. Amma an hukunta shi ne domin ya zama izina ga sauran Yan Majalisar.
Ya ce hakan zai sa kowannen su ya rinka yin abun da ya dace don kare martabar ita kanta Majalisar.
Ya ce shi bai ga bayanai da Abdul Ningi ya ke ikirari ba. Sabo da haka ba shi da wata hujja da zai ce ya gani.
” an ce akwai bayanai amma ba a nuna mana su ba. Sai mu ce mun gani”.
Majalisar Dattawan dai ta dakatar da Sanata Abdul Ningi da ga Majalisar na tsawon watanni uku bayan da aka gudanar da zazzafar mahawara akan zargin da ya yiwa Majalisar cewa akwai kudi kimanin Naira Tiriliyan uku da ba a jingina su da wani aiki ba a kasafin kudi na 2024.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here