Home Lafiya Lafiya Ga Mata Ma Su Ciki Kyauta: Majalisar Wakilai Ta Umarci Ministan...

Lafiya Ga Mata Ma Su Ciki Kyauta: Majalisar Wakilai Ta Umarci Ministan Lafiya Da Ya Baiyana A Gabanta

111
0
Hon. Dan Abba Zaki

Majalisar Wakilai ta umarci Ministan Lafiya, Muhammad Ali Pate da ya baiyana a gabanta domin ya yi bayani akan dalilin da ya sa  mata ma su ciki ba sa amfana da shirin Gwamantin Taraiya na ba su magani da kulawa kyauta a lokacin haihuwa.

Majalisar ta bayar da wannan umarni ne bayan da Dan Majalisar, mai Wakiltar karamar Hukumar Zaki da ke Jihar Bauchi, Hon. Muhammad Dan Abba Shehu, ya gabatar da Kuduri na gaggauwa akan yadda mata su ke  rasa rayukan su sakamakon rashin ba su kulawa ta musamman a asibitoci na Gwamnatin Taraiya da su ke Kasarnan.

Hon. Dan Abba cewa ya yi dalilin sa na gabatar da wannan Kuduri shi ne ya lura da yadda mata su ke shan wahala lokacin haihuwa musamman ganin yadda asibitoci su ke kin ba su kulawa ta gaggawa duk da cewa Gwamnati Taraiya ta bayar da umarnin cewa kulawa da mata ma su juna biyu kyauta ne a asibitocin ta.

Ya ce ya na da masaniya cewa a kasafin kudi na Ma’aikatar Lafiya ta Gwamnatin Taraiya a na ware makuden kudade domin tallafawa mata ma su ciki kyauta amma abun mamaki ba’a aiwatar da wannan umarni.

Bayan haka ya kara da cewa har ila yau, ya na da masaniya cewa akwai kungiyoyi na kasashen waje da su ke tallafawa da makuden kude domin a kula da mata ma su juna biyu musamman lokacin renon ciki da kuma haihuwa.

A  daya bangaren kuma, ya lura kwarai da gaske yadda matsi na tattalin arzikin Kasa ya jefa da yawa na ma su gidaje wadanda da kyar su ke iya ciyar da iyalan su; barantana kuma a ce su samar da kudade da ake bukata na asibiti.

Ya ce rashin samun kulawar da mata ma su ciki su ke yi, ya yi sanadiyyar mutuwar mata ma su yawa a Kasarnan. In da ya ce dakan sa ya ke zaga yawa asibitoci da su ke yankin sa duk lokacin da ya koma gida; hakan ta sa yaga abubuwan tashin hankali, shi ya sa , ya gabatar da Kudurin.

Hon. Dan Abba ya nuna jin dadin sa da Majalisar ta amince da wannan Kuduri na sa; musamman yadda yan uwansa Yan Majalisa su ka ba shi goyon bayan, wanda hakan ya sa Majalisar ta amince da Kudurin ba tare da wani bata lokaci ba.

Ya ce a na saran Ministan zai baiyana a gaban Kwamitin Lafiya na Majalisar Wakilai nan da sati biyu ma su zuwa domin ya yi bayani na dalilin da ya sa ba’a aiwatar da Dokar kulawa da mata ma su ciki kyauta a asibitocin Gwamnatin Taraiya.

Da ga karshe Dan Majalisar ya yi kira da Gwamnoni da Shugabannin Kananan Hukumoni da su ma su tabbatar da cewa ana kulawa da mata ma su ciki Kyauta a Jihohi da kananan Hukumomi domin rage yawan mace-mace da ake fuskanta sakamakon rashin kulawa ta musamman ga mata ma su ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here