Home Cinikaiyar Zamani kyale yadda kasuwar dala take: Da na ga dama, ni ma da...

kyale yadda kasuwar dala take: Da na ga dama, ni ma da na amfana amma na ce a’a – Shugaba Tinubu

199
0
Naira and Dollar

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana a wani taro a Legas cewa da ya so da ya kyale yadda cinikin canjin Dala ya ke daban daban ciki da waje, don shima ya amfana da harkallar.

” Amma da ya ke hakan ba shi ne abin da mutane suka zabe mu mu yi ba, gyara muka zo yi ya sa, na ce a maida kowannen su daidai ci da waje.

Tinubu ya ƙara da cewa dole gwamnati ta yi gaggawar toshe duk wata da za a rika waftar arzikin kasa ba tare da talaka ya amfana ba, da shine ya sa mu ka soke biyan kuɗin tallafin mai, domin mu samu kuɗin gina kasar mu.

” Gwamnatin mu na kowa da kowa na, muna maraba da duk wata shawara da za a bamu domin ci gaban kasar. Kofofin mu a buɗe su ke.

Daga nan sai ya roki wasu abokan sa da suka yi ta kokarin su gan shi amma abin ya gagara saboda yanayi aikin da ya sa a gaba na shugabancin Najeriya.

” Ku yi hakuri da ni, yanzu ba loka ci ne da zama a falo a na shan shayi ba, lokaci ne na aiki. Ayyukan da yawa. Amma ina nan tare da ku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here