Home Siyasa Kwankwaso: Muna Magana Da Tinubu Kan Shiga Gwamnatin Sa

Kwankwaso: Muna Magana Da Tinubu Kan Shiga Gwamnatin Sa

231
0

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu ya yi masa tayin muƙami a gwamnatinsa, sai dai ya ce har yanzu ba su kai ga cimma matsaya ba.

Sanata Kwankwaso ya bayyana haka ne lokacin da ya ke yi wa BBC karin bayani kan ganawar da suka yi da shugaban kasar a jiya Juma’a ta kimanin sa’a biyu.

Tattaunawar na zuwa ne adaidai lokacin da dambarwa ke sake kamari tsakanin ɓangaren sabuwar gwamnatin Kano da kuma gwamnatin APC da ta shuɗe.

Sai dai da alama tattaunawar tsakanin Kwankwaso da Tinubu na sake nuna kyakyawan alaƙa da mara-baya da NNPP ke iya samu daga bangaren gwamnatin Tarayya.

Kwakwaso dai ya ce daga cikin abubuwan da suka mayar da hankali a ganawar akwai abinda ya shafi harkokin siyasa da harkoki na gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here