Home Siyasa Kungiyoyin Matasan Arewa Sun Roki Ministan Abuja, Wike Da Ya Bar Jam’iyar...

Kungiyoyin Matasan Arewa Sun Roki Ministan Abuja, Wike Da Ya Bar Jam’iyar Sa Ta PDP Ya Koma APC

92
0
Arewa Group 2

Gamaiyar Kungiyoyin Matatasan Arewa sun roki Ministan Babban Birnin Taraya Abuja, Nyensom Wike da ya yi kaura da ga Jam’iyar sa ta PDP ya koma Jam’iya mai mulki ta APC sakamakon irin aikace-aikace da ya yi a cikin shekara guda wanda hakan ya nuna cewa shi dan kishin Kasa ne mai son cigaban Najeriya.

Wannan kira ya zo ne a lokacin da Kungiyoyin su ka shirya taron Yan Jaridu wanda ya gudana a dakin taro na Mungo Park da ke birinin Taraiya Abuja a ranar Alhamis.

Wanda ya yi jawabi a maimakon Gamaiyar Kungiyoyin, Shugaban Kungiyarnan na Yan Arewa ma su rajin kawo Kyakkyawan Canji wato NYMPC, Komared Isyaka Babanagode cewa ya yi dalilin su na kiran Wike da ya bar Jam’iyar sa ta PDP ya koma APC shi ne sun lura cewa shi, jinin APC ne a jikin sa lura da irin aiyukan da ya gudanar a matsayin sa na Ministan Abuja a cikin shekara daya duk da cewa shi da ga jam’iyar adawa ya ke.

Babanagode ya ce, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu wanda ya nada shi a matsayin Minista duk da cewa shi ba dan Jam’iyar APC ne a matsayin sa na mai son cigaba; ta tabbata a fili cewa sun hadu a akida ta nuna son Kasa da Kishin ta, shi ya sa suka ga cancantar da ya dawo jam’iyar domin ya cigaba da bayar da gudunmawa wajen gina Kasarnan.

Ya ce irin aikace aikace da Wike ya yi a cikin Shekara guda a Abuja sun nuna karara irin kyakkyawar zuciya da ya ke da ita ta cigaba. In da ya zaiyana irin aiyukan da ya aiwatar kamar sabunta tituna sama da guda 100 da gyara makarantu da gina titin jirgin Kasa da samar da wutar lantarki da kammala gadji musamman ta unguwar Wuye da sauran manyan aiyuka.

Jagoran Kungiyoyin ya ce, a bangaren samar da Tsaro ma a birinin Taraiyar, Minista Wike bai yi kasa a gwiwa ba domin ya samar da ingantaccen tsaro tare da bawa hukumomin Tsaro kayan aiki na zamani da motoci a wani mataki na ganin an samar da zaman lafiya da cigaba a birnin.

A bangaren yakar Cinhanci da Rashawa ma, Babanagode cewa ya yi, Wike bai yi wata-wata ba wajen daukar matakai na ganin ya dakile su a birnin ta hanyar saka ido da bin diddigi na ganin an gudanar da aikin gwamnati cikin doka da tsari.

Gamaiya Kungiyoyin su ka ce a bisa wannan dalili ne su ka ga dacewar na da su gaiyato Ministan Abujan da ya gaggauta barin Jam’iyar sa ta PDP domin bata dace da shi ba, ya koma Jam’iyar APC, ita tafi dacewa da shi domin jam’iya ce da aka gina ta da akidu da su ka yi daidai da irin akidu da shi Wike ya ke da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here