Home Siyasa Kungiyar COAD Ta Soki Yunkurin Mayadda Takarar Shugaban Majalisar Dattawa Zuwa Kudu

Kungiyar COAD Ta Soki Yunkurin Mayadda Takarar Shugaban Majalisar Dattawa Zuwa Kudu

201
0

Wata Kungiya mai rajin kare martabar Demokradiyya mai suna “Coalition for Advance Democracy (COAD)” da ke da mambobi daga Jihohi 36 har da Abuja ta ne mi da a bawa yankin Arewa maso Yamma da ma da ya fidda gurbin Shugaban Majalisar Dattawa  a Majalisa ta Goma du ba da ganin irin gudunmawar da yankin ya bayar a zaben da ya gabata na 25 ga watan Fabrailu.

Kungiyar na maida martani ne ga kalaman wani mataimakin Shugaban Jam’iyar APC na Kasa daga Yanki Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya yi na cewa bai kamata yankin Arewa maso Yamma ya ce yana bukatar mukamin Shugaban Majalisar Dattawa ba.

Kungiyar ta ce bukatar da yankin Arewa maso Yamma ya ke yi na shugaban Majalisar Dattawa bai sabawa kundin tsarin mulki na Jam’iyar APC ba kuma bai sabawa Kuddin tsarin mulki na Kasa ba.

A wani taro na gaggawa da kungiyar ta gudanar a Abuja karkashir jagorancin shugaban kungiyar, Malam Yousouf Zulkiflu tace ba da dai bane ace Arewa maso Yamma ba zata fito da dantakarar shugaban majalisar Dattawa ba a Majalisa ta goma.

Zulkiflu ya gabatar da hujjoji da suka nuna chanchantar Arewa maso Yamma na da ta fidda Shugaban Majalisar Dattawa duba da irin gudunmawar da ta bayar a zaben da ya gabata wanda ya bawa dantakarar Shugaban Kasa na Jam’iyar APC Bola Ahmad Tinubu da Kashim Shettima nasara a zaben.

Yace yanki ya bayar da gudunmawar kuri’u da suka fi na kowanne yanki., wanda itace hujja mafi girma da ke nuna chanchantar yankin na da ya fidda shugaban Majalisar Dattawa.

“kalaman mataimakin shugaban Jam’iya na yankin Arewa maso Yamma, na Salihu Lukman sunyi mutukar sosa mana rai kuma sun kauce al’adar jam’iyar APC da duk wani ma’auni na siyasa wajen nuna chanchantar tsayawar takarar shugabancin Majalisar Dattawa ta Kasa” inji Zulkiflu.

Ya kara da cewa Arewa maso Yamma ita tafi chanchanta na ta fidda Shugaban Majalisar Dattawa a majalisa ta goma sabo da dalilai kamar haka: ta bayar da kaso 30 na kuri’u da aka kada a zaben da ya gabata; “ to me nene hujjar Lukman na cewa a kai mukamin shugaban Majalisar Dattawa Kudu wanda Yankunan guda biyu gudunmawar da suka bayar shine kaso 1.45 da kaso 9.10 kacal a zaben shugaban kasa da ya bawa Bola Ahmad Tinubu da Shettima nasara”

Zulkiflu yace jam’iyar APC ba ta yi adalci ba idan ta kai takarar Shugaban Majalisar Dattawa yankin Kudu sabo da basu bayar da gudunmawar da ta chanchanta ba a Siyasa.

“ Ya kamata a binciki Mr. Lukman domin gano wanda ya kewa aiki. Shin laifi ne bayar da gudunmawar kuri’u masu yawa domin kawo nasarar jam’iya a lokacin zabe? Me nene laifin yankin Arewa maso Yamma na ruwan kuri’a da ya kawo nasarar Bola Tinubu da Shettima? Zulkiflu ya tambaya.

Jagoran Kungiyoyin yace, Mr. Lukman ya yi kuskure kuma ya kuskure lissafin siyasa da ya faru a kasarnan inda ya bayar da tarihin yadda jam’iyar NPN ta fidda shugabanni a shekara ta 1978 inda Shugaban Kasa Musulmi, Mataimakin Shugaban Kasa Kirista, Shugaban Majalisar Dattawa Kirista, Shugaban Majalisar Wakilai Kirista da shugaban Jam’iya Alhaji Alani Bankole dukkaninsu da ga yanki kudu.

Sabo da haka ya zama wajibi a wannan karon ma a baiwa yankin Arewa maso Yamma da ma na ya fidda Shugaban Majalisar Dattawa sabo da irin gudunmawar da ya bayar wajen samun nasarar jam’iyar APC a zaben shugaban kasa da ya bawa Bola Ahmad Tinubu da Shettima nasara.

Kungiyar tace a wannan bigire, mutumin da ya fi chanchata da ya zama Shugaban Majalisar Dattawa shine Abdul’ziz Yari domin yafi kowa chanchanta duba da irin gudunmawar da ya bayar a siyasance.

Kungiyar ta yi kira ga uwar Jam’iyar APC ta kasa da ta yi watsi da kalaman Mataimakin Shugaban Jam’iyar APC na yankin Arewa maso Yamma Mr. Lukman ta bawa Yankin Yankin Arewa maso Yamma damar fidda Shugaban Majalisar Dattawa a Majalisa ta Goma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here